Daga - Muhammad Attahiru
A wani biki da aka gudanar shekaran jiya Lahadi a Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i ya amince da Masoud Pezeshkian a matsayin shugaban ƙasar na tsawon shekaru huɗu a hukumance.
Amincewar ta gudana ne kwanaki biyu kafin rantsar da Pezeshkian a majalisar dokokin ƙasar tare da halartar wakilai 70 na kasashen waje da suka haɗa da shugabanni da firayim minista goma.
A cikin wani saƙo da daraktan ofishin Jagoran ya karanta, Ayatullah Khamenei ya ce: "Ina goyon bayan ƙuri'ar da aka kaɗa ga mai hikima, gaskiya, shahararre kuma malami Mr. Pezeshkian, kuma ina naɗa shi a matsayin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran."
Bikin ya samu halartar manyan jami'an ƙasar Iran da suka haɗa da shugaban ma'aikatar shari'a, shugaban majalisar dokoki, shugabannin majalisar kwararru da majalisar kula da harkokin tsaro, manyan jami'an siyasa da soja da shugabannin jam'iyyar da kuma jami'an diflomasiyyar ƙasashen waje da ke zaune a Tehran.
Dokar majalisar ta tanadi cewa, sabon shugaban ƙasar ya gabatar da tsare-tsarensa tare da gabatar da ministocinsa cikin makonni biyu bayan rantsar da shi. Ga cikakken bayanin hukuncin da ke tabbatar da shugabancin Pezeshkian, wanda Ayatullah Khamene'i ya fitar a ranar 28 ga Yuli, 2024:
"Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Muhammadu, da Alayensa tsarkaka, musamman ma sauran bayin Allah a bayan ƙasa."
"Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin Sarki mai kowa mai komai, domin kuwa ya sake ƙara daukaka ga Iran ɗin Musulunci da haskaka fuskokin wannan al'umma mai girma."
"Tare da ƙoƙarin jama'a da jami'ai, an gudanar da jarrabawar zaɓen shugaban ƙasa cikin kwanciyar hankali ƙarƙashin yanayi mawuyaci, sannan wanda al'ummar ƙasar suka zaɓa a yanzu a shirye yake ya dauki babban nauyi.
A yanzu da nake godiya ga duk waɗanda suka taka rawa wajen samar da wannan karramawa bisa ga ra'ayin al'ummarmu mai girma, ina goyon bayan kuri'arsu ga mai hankali, mai gaskiya, mai kishin jama'a kuma masani Dr. Masoud Pezeshkian, don haka ina mai naɗa shi a nan a matsayin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Da wannan nake addu'o'i tare da fatan samun nasara, ina kuma tunatar da cewa, ƙuri'ar al'umma da amincewata za su ci gaba da wanzuwa muddin tsarinsa na bin tafarkin Musulunci da juyin juya hali.
©️ Freedom Fighters Hausa Ng🎙️
0 Comments