Daga - Mahadi Tukur Almizan
A halin da ake ciki yanzu miliyoyin Palasɗinawa ba su da muhalli sakamakon ci gaba da ta'addanci da sojin Isra'ila ke yi zirin Gaza.
A yau 24 ga watan July ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam 'Euro-Med Human Rights' ta bayyana cewa ta'addancin Isra'ila a birnin Khan Yunis yana daga cikin hare hare mafiya muni da suka faru tun daga fara wannan yaƙi.
Kafar yaɗa labarai ta The Monitor ta bayyana cewa ƙazaman hare haren da suke faruwa a Khan Yunis sun yi sanadiyyar shahadar aƙalla Palasɗinawa 89 wasu sama da mutum 263 sun samu raunuka, kuma wannan adadin zai cigaba da karuwa kowane lokaci.
Wakilin kafar yaɗa labarai ta Aljazeera a tsakiyar Gaza ya bayyana cewa sojin na Isra'ila sun hana ma'aikatan lafiya zuwa kai ɗauki bayan sun ƙaddamar da mummunan hari a gabashin birnin Khan Yunis.
Ɗan jaridar ya kara da cewa mutane a Khan Yunis sun rasa inda za su je, suna ta yawo babu mafaka, sakamakon hare haren Isra'ila a kowane lungu da saƙo na birnin.
This is how the displaced families from eastern Khan Yunis slept tonight in Nasser Hospital. There is no safe place in Gaza and no room for the displaced 😐😐 pic.twitter.com/jctqlIgKzQ
— Kareem 🇵🇸🇵🇸🇵🇸 (@Kareem802329280) July 24, 2024
A halin yanzu asibiti guda ɗaya tilo da ya rage a birnin na Khan Yunis ya cika maƙil da masu raunuka, hukumomin asibitin su nata neman agajin jini domin kulawa da masu raunuka da ake cigaba da kawowa asibitin.
Sojin na Isra'ila sun sake afkawa kudancin birnin bayan wa'adin barin birnin da suka bayar na ƙasa da sati biyu, wanda ya tilasta Palasɗinawa barin birnin Gaza, aƙalla Palasɗinawa dubu 150 sun bar Khan Yunis basu da mafaka kamar yadda Aljazeera ta wallafa.
Ofishin kula da harkokin bada agaji na majalisar ɗinkin duniya 'OCHA' ya gargaɗi bisa yanayin da ake ciki kamar yadda suka wallafa a ranar Litinin 22 ga watan July cewa kusan kaso 83 na mutanen Gaza sun bar muhallan su kamar yadda Isra'ila ta tilasta masu barin muhallan inda ta kira 'no go zones'.
A na su bangaren rundunonin ƴan muqawama na Palasɗinawa suna cigaba da kaima sojin Isra'ila hare hare a yankunan birnin Khan Yunis.
Rundunar Qassam Brigades ta sanar da cewa takai hare hare mabanbanta kan tankokin sojin Isra'ila da motocin da suke rusa gidajen Palasɗinawa tsawon kwanaki 2 a gabashin birnin Khan Yunis.
0 Comments