Daga - Mahadi Tukur Almizan
Sojin Isra'ila sun aikata kisan kiyashi a sansanin Palasɗinawa ƴan gudun hijira da ake kira "Nuseirat Camp".
A shekaranjiya asabar ne sojojin Isra'ila suka jefa boma bomai a makarantar hukumar majalisar ɗinkin duniya dake baiwa Palasɗinawa agaji 'UNRWA, wannan makaranta ta zama wurin zaman Palasɗinawa masu yawa sakamakon raba su da muhallan su.
Mata da Yara da Mata ne dai suke rayuwa a wannan makaranta da ake kira al-Jaouni, mutum 16 ne suka rasa rayukansu sakamakon wannan boma bomai da sojin na Isra'ila suka jefa sannan wasu mutum 50 suka samu raunuka.
Bangarorin ƴan Muqawama na Palasɗinawa sun yi Allah wadai da wannan kisan ta'addanci na Isra'ila.
Ƙungiyar Hamas ta yi Allah wadai da wannan ta'addanci na sojin Isra'ila a wannan makaranta da ta zama wurin rayuwar dubunnan Palasɗinawa.
Hakanan kungiyar 'Popular Front For The Liberation Of Palestine' (PFLP) ta yi Allah wadai da wannan ta'addanci na Yahudawan Sahayuniya kan raunana.
Wannan hari shine na 43 da Isra'ila ta kai wannan sansani tun daga 07 October.
A baya bayan nan a ranar 8 ga watan June Isra'ila ta kai harin da ta kashe mutum 274 a rana ɗaya a wannan sansani na Nuseirat karkashin rundunar 'Yamam Commando Units' sun kashe Palasɗinawa 274 sun karbo mutanen su Isra'ilawa 4.
Gaza Ministry of Health says 274 Palestinians killed and 698 injured by Israel during the Nuseirat camp massacre, carried out to rescue four Israeli captives. pic.twitter.com/nbv41rByG9
— The Cradle (@TheCradleMedia) June 9, 2024
Shaidun gani da ido sun bayyana yadda suka ga munanan hare haren ta'addancin Isra'ila, akwai ranar da suka kai hari mutane na bacci suka harba rocket guda 150 a cikin kasa da mintuna 10 suka lalata unguwa baki ɗayan ta.
Wani daga cikin mazauna unguwar mai suna Abu Abdallah ya bayyana ma kafar yaɗa labarai ta CNN cewa "Muna gani karnuka na cin naman mutanen da suka mutanen da suka mutum, haka muka yi kokari muka iya daukar shahidai 6 daga ciki dukkanin su Yara ne da Mata, haka muka sadaukar da rayuwar mu muka kai su asibiti".
Hakanan a ranar 16 ga watan March jirgin yaƙin Isra'ila ya kai hari a sansanin inda ya kashe mutum 36 ƴan gida ɗaya da suka taru suna buɗe baki bayan shan ruwa na azumin watan Ramadan.
Wani bafalasɗine mai suna Mohammed al-Tabatibi mai shekaru 19 ya nuna ma wakilin kafar yaɗa labarai na AFP yadda jikkunan iyalan gidan su suka yi watsa watsa a asibitin Al-Aqsa Matyrs Hospital dake kusa da Deir al-Balah.
A cikin bidiyon yana nuna ma ɗan jaridar cewa "Wannan shine Mahaifina, wannan itace Mahaifiyata, wannan itace gwaggo ta waɗancan ƴan uwa na ne" wannan fa gawarwakin su yake nuna wa sunyi kaca kafa yana nunawa yana kuka.
Ya bayyana cewa "Sun jefa ma gidanmu Bomb, a lokacin Mahaifiyata da Auntyna suna shirya abincin Sahur, duk an kashe su".
Hakanan a ranar 20 ga watan Octoy Isra'ila ta jefa Bomb a gidan al-Aydi dake sansanin na Nuseirat inda suka kashe mutum 28 ciki da Yara 12.
Wani rahoto na ƙungiyar Amnesty International ya bayyana cewa mutanen da suka mutu a gidan sun hada da Rami al-Aydi da matar shi Ranin, da ƴaƴansu guda 3 Ghina,Ten da Mata, da Iyad su shida duk an kashe su, hakanan Zeina Abu Shaheda da ƴaƴanta 2 duk an kashe su Amir al-Aydi da Rakan al-Aydi, hakanan an kashe mamar Zeina da ƴan uwanta biyu.
Hani al-Aydi shi kadai ya rage ya bayyana ma Amnesty cewa "Muna zaune a gida Muna zaune mu dayawa ƴaƴa da ƴan uwa kwatsam sai mukaji gidan ya ruso kan mu, duk ƴan uwa na da kawunnai na da ƴaƴan su da Mama da ƴan uwa na Mata duk sun mutu gidan yatafi babu abinda ya rage".
0 Comments