Ministan Isra'ila Mai Tsatsauran Ra'ayi ya yi kira da a Sake Mamaye Kudancin Lebanon

 


Daga - Muhammad Attahiru

Ministan kudi na Isra'ila mai ra'ayin riƙau, wato Smotrich ya yi kira cewa a sake mamaye yankin kudancin ƙasar Lebanon a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun saƙa tsakanin gwamnatin ƴan ta'adda da ƙungiyar Hizbullah. 


A yayin jawabin da ya yi a tsohon birnin al-Quds da aka mamaye a ranar Litinin, Bezalel Smotrich ya ba da hujjar cewa yaƙi da Hizbullah ne kawai zai iya sassauta rikicin, yana mai karawa da cewa, "Al'ummar Isra'ila a shirye suke da hakan." 


Ministan wariyar launin fata ya ci gaba da cewa, "Babu wata hanya ta maido da tsaro ga mazauna arewacin ƙasar ba tare da yaƙin da zai ruguza kungiyar Hizbullah ba, wanda zai sake mamaye kudancin ƙasar Lebanon." Ya kuma kara da cewa, dole ne Isra'ila ta samar da wani shingen tsaro a cikin ƙasar ta Lebanon.


Isra'ila dai ta mamaye wani yanki na kudancin Lebanon ne a farkon shekarun 1980 sannan ta fice daga yankin a watan Mayun shekara ta 2000. Kalaman da Smotrich ya yi mai cike da cece-kuce ya zo ne kwanaki biyu bayan da wani makamin roka ya afkawa filin wasan kwallon kafa a garin Druze na Majdal Shams a yankin Syria da Isra'ila ta mamaye. Tuddan Golan, wanda ya kashe mutane 12, yawancinsu yara kanana.


Hizbullah a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce "ba ta da alaƙa da lamarin, kuma ta musanta dukkan zarge-zargen ƙarya game da hakan." Wasu rahotanni sun bayyana cewa mai yiwuwa lamarin ya faru ne sakamakon wani makami mai linzami da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta harba da makami mai linzami da ake kira Iron Dome.


A halin yanzu ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Siriya ta ce Isra'ila ce ta aikata wannan danyen aikin a Majdal Shams a wani bangare na yunkurinta na kara ruru wutar halin da ake ciki da kuma faɗaɗa iyakokinta na kisan gillar da take yi wa yankin na Gaza da kungiyar Hizbullah da Isra'ila ke ta musayar wuta da juna tun a farkon watan Oktoba. 


Jim kaɗan bayan da gwamnatin ƙasar ta kaddamar da mummunan yakin da take yi a zirin Gaza, bayan wani harin ba-zata da ƙungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta kai ta sha alwashin ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya muddin gwamnatin Tel Aviv ta ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza, wanda kawo yanzu ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 39,363, galibi mata da ƙananan yara, tare da raunata wasu 90,923. 


Wasu kafafen yaɗa labaran Isra'ila sun ce hare-haren ramuwar gayya na kungiyar Hizbullah ya raba kusan mazauna 60,000 da muhallansu a Isra'ila daga yankunan arewacin da aka mamaye.



Allah ya kawo ƙarshen duk wani zalunci da azzalumi ya kuma zaunar da wannan duniya lafiya.


___ Freedom Fighters Hausa Ng🎙️

Post a Comment

0 Comments