Daga - Mahadi Tukur Almizan
Haramtacciyar ƙasar Isra'ila na riƙe da aƙalla Palasɗinawa 10,000 a gidajen yari da wasu wuraren tsare mutane a cikin Isra'ila inda suke azabtar da su.
A jiya Lahadi 30 ga watan June da ya ƙare kafar yaɗa labarai ta WAFA ta labarto cewa ministan tsaron ƙasa na Isra'ila mai suna Itamar Ben Gvir yayi kira da cewa a fara hukunta fursunonin na Palasɗinawan da Isra'ila ke tsare da su a gidajen yari.
A cikin bidiyon da aka wallafa Ben Gvir ya bayyana cewa yakamata Isra'ila ta hukunta fursunonin Palasɗinawan ta hanyar harbin su da bindiga a kai.
Ya nemi a gaggauta shigar da wannan bukata zuwa majalisar haramtacciyar ƙasar da ake kira 'Knesset' domin a fara yin wannan hukunci.
Ben Gvir ya kara da cewa a baiwa fursunonin isasshen abinci domin su kasance a raye zuwa lokacin da majalisar zata tabbatar da wannan buƙata a matsayin doka.
Tun a farkon watan March na shekarar 2023 majalisar ta karbi bayanan wannan bukata.
Bukatar ta nemi majalisar ta zartar da kisa ya zama shine hukuncin duk wani bafalasɗine da ya hari ƴan mamaya, dokar ta shafi waɗanda suka kashe ƴan mamaya wanda ƙyamar Isra'ila ke haifar wa, kuma hakan na cutar da ƙasar ta Isra'ila, kamar yadda suka bayyana a kudurin dokar.
BREAKING | Israeli National Security Minister Itamar Ben-Gvir calls for Palestinian prisoners to be shot in the head, saying he plans to pass legislation in the Knesset that would allow for the execution of Palestinian prisoners, who "must be killed." pic.twitter.com/xxcIUIiWHo
— The Cradle (@TheCradleMedia) June 30, 2024
A cikin watan April Ben Gvir yayi kiran a fara kashe Palasɗinawa domin a rage cinkoson gidajen yarin Isra'ila.
Tun daga October na shekarar 2023 kamen da Isra'ila ke yi ma Palasɗinawa ya ta'azzara.
Ƙungiyar kamammun Palasɗinawa "Palestinian Prisoners Association" ta bayyana ma kamfanin dillancin labarai na Reuters a watan da ya gabata cewa Isra'ila ta kama aƙalla Palasɗinawa 9,170 a West Bank daga 07 October zuwa yau a cewar ƙungiyar "Da ƙarfi da yaji Isra'ila ta ɓatar da wasu dubunnai daga kuma taƙi bari asan adadin mutanen da ta kama".
A kwanakin baya da aka sako wani daga cikin Palasɗinawan mai suna Ataa Shabat ya bayyana cewa "Mu dai mun fito, amma muna kira kuyi kokari ku fito da saura", ya kara da cewa dayawa daga cikin wadanda ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila sun yi amanna cewa ƴan uwan su sun ɗauka sun mutu.
"Mutane suna mutuwa sanadiyyar azabtarwar da ba zaka iya misaltawa ba, in har ba ka ɗanɗana ta ba, ana wahalar da ba zaka iya sawwalawa ba" a cewar Ataa.
Kungiyar ta Palestinian Detainees Association ta bayyana cewa aƙalla mutum 18 suka rasa rayukansu a gidajen yarin Isra'ila tun daga fara yaƙin na Gaza.
0 Comments