Daga - Shamsudeen Hassan
Yanzu gwajin Ƙarfi ne ake na kusurwa Ukku (triangle). Gwamnati, Talakawa da bara Gurbin malamai. Duk wanda yayi Nasara to Power za ta dawo hannunsa a nan gaba. Kowanne daga cikinsu muradunsa yake kokarin karewa a yanzu, kuma kowane daga cikinsu bayada tabbacin yin Nasara. Har sai an gwabza.
Idan talaka ya murje yaudarar Malalamai, ya fita ya gwada ƙunjinsa wajen Kwatar yanci. To a nan gaba zai iya yiwa gwamnati tsawa ta saurareshi.
Idan kuwa malamai su suka yi Nasarar ƙara jefa Talakawa baccin gafala, to a nan gaba za su fara shatawa Gwamnati dokokin biyawa kansu muradunsu na Ƙungiyanci kuma dole ta sauraresu.
Idan kuwa gwamnati ta yi Nasarar wautar da Talakawa da Alkawullan karya kuma suka yadda suka kwanta, to nan gaba sai sun rasa matsugunni, sai sun rasa abinci, sai sun rasa, gona, sai sun rasa hatta irin shuka, sai sun rasa magani, sai sun rasa yancinsu na zamansu mutane, sai su rasa Yancin faɗin ra'ayi.
Najeriya ta na cikin kusurwa Ukku ne. Ɗauki ba daɗi ne an riga an farashi.
Duk wanda yayi Nasara to shine zai baza capacity a shekaru masu zuwa.
Rubutu na biyu 👇
A gaida Talakawa, aikinku ya fara kyau. Karfinku ya kusa dawowa a hannunku, dama naku ne. Asalin karfi yana hannun al'umma ne, ba hukuma ko masu rike da bodojin Addini ba.
Dama sani ne ba a yi ba. Duk al'ummar da ta san haka, kuma ta ɗanɗana to ta wuce wulakanci har abada.
Yanzu dai an murɗe wuyan Malamai. Ba a wurgosu daga kan mumbari ba, amma an tirsasu dole Darasi ya canja. Idan muka ce malamai muna nufin zauna gari banzan da suka kasa samun aikin yi suka ari rigar malamai suna Business da ita. Muna nufin raggayen gari, matsorata, masu Sayarda mutuncinsu dana al'umma domin su samu na cimaka. Ba Malamai yana Allah ba, wadanda ke zaune a soro da zauruka da Jami'o'i da cibiyoyin ilimi suna fitowa da Jauharin Ilimomi. Haka ba malamai na gari, masu kokarin kwatowa Raunana hakkinsu ba. 'Yan KEDCO masu nadi a saman kai.
Su kam wadannan yanzu Talakawa sun bi ta kansu sun murje. Daga cikinsu akwai wadanda dole sun ja baki sun yi shiru, akwai wadanda sun dawo sukar hukuma dole, domin gudun kada Business center ta zamo empty. Akwai waɗanda sun dawo jinjinawa Talakawa tare da raba kafa. Akwai waɗanda suka sauya ra'ayi suka ce ana iya yi. Akwai kuma kangararru har ynz basu ji bugu ba. To ku bi ta kansu. Ku Nomesu a ciki da wajen, ku yakice shagunansu. Cuta ne su a cikin Al'umma.
Yanzu inda yakin yafi zafi, shine tsakanin al'umma da yan siyasa, su kuma yan siyasa dama matsorata ne, ku ne kayan sayarwarsu. Idan kun bijire sakin kari za su yi. Yanzu haka ma sun fara sakin kari. Sun fara sassautawa. To a rike wuta, kar a yi reverse. Idan sun ji wuta za su yi babbar saranda.
Idan wannan kokawa ta kare, ya zamo tallaka ne yayi nasara, to shikenan, hanya ta bulle.
Yanzu abunda ya rage, sai a yi karatun ta natsu a gano shin wai tun asali, daga ina ne matsalar na take fitowa.?
Minene tushenta? Ya za a yi a maganceta?
Tushe matsalar dama yana daga abunda aka danƙara mana ne, a matsayin tsarin mulki, wanda bai dace da Addini da aladunmu ba.
To shi za mu haɗu mu yakice, sai mu sauyashi da waninsa mai kyau.
Don haka, idan an gama kwato tuwo, to a zo a haɗu a kwato yanci, a kwato, Mutunci, a kwato addini. Idan ba haka ba, to a nan gaba ba tuwo kadai zai gagari talaka ba, har da Kasar gaba Ɗaya.
Shamsudeen Hassan Zuru
30/7/2024
13/7/2024
0 Comments