Sama Da Mortar Shells 200 Ƴan Muqawama Suka Harba Hedikwatar Sojin Isra'ila Ta Mashigar Netzarim: An kwashi gawarwaki Da Masu Raunuka

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Isra'ila ce da kanta ta bayyana cewa An kashe sojojin ta biyu a tsakiyar zirin Gaza a jiya 2 ga watan July.


A jiya Talata rundunar sojin Isra'ila ta sanar cewa daga ranar Lahadi zuwa Litinin an raunata sojojin ta har guda 44 kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Almayadeen ta wallafa a shafin su na Larabci.


Kafar yaɗa labaran Isra'ila mai suna Ynet ta wallafa maganar da mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila yayi a jiya Talata yana cewa " An kashe Major Eyal Abneon da Sergeant Major Nadav Elhanan Noler  ta hanyar dasa abun fashewar a mashigar Netzarim" da ake kira 'Netzarim Corridor' ya kara da cewa ana kan binciken faruwar lamarin.



Rahota Palestine Chronicle sun tabbatar da cewa a shekaranjiya Litinin ƴan gwagwarmaya na Palestinu suka kai mummunan hari kan sojin na Isra'ila a mashigar ta Netzarim da ta raba zirin Gaza gida biyu dake kusa da tsakiyar Gaza.


A ranar ta Litinin 1 ga watan July kafar yaɗa labaran Isra'ila 'Hebrew Media" ta labarto cewa wani gagarumin al'amari ya faru a mashigar Netzarim a yammacin ranar ta Litinin inda aka ga Helicopter na sojin Isra'ila ya sauka yana kwashe sojojin da suka samu raunuka, ya ɗauke su zuwa wata asibiti a Beersheba mai suna 'Soroka Hospital'.


Kafar yaɗa labarai ta 'Israel' Without Censorship' ta bayyana cewa an kai wasu sojojin wasu asibitoci daban daban.


Hakanan Daraktan kafar yaɗa labarai ta Almayadeen Nasser al-Lahham ya tabbatar da cewa an kai sojojin da suka samu raunuka asibitin Assuta dake Ashdod da Soroka Hospital dake Beersheba a ranar ta Litinin.


Nasser ya ƙara da cewa dakarun rundunar 99th Division ne suka nemi agajin akawo masu ɗauki ta sama sakamakon faruwar wani ƙazamin hari a mashigar ta Netzarim.



Wannan mashiga ta Netzarim dai tana fuskantar hare hare daga rundunonin ƴan gwagwarmaya na Palasɗinawa mabanbanta, Qassam Brigades,Quds Brigade, Al-Aqsa Matyres Brigade da sauran su.

Post a Comment

0 Comments