Daga - Mahadi Tukur Almizan
Aƙalla Palasɗinawa 90 ne suka rasa rayukansu wasu mutum 300 kuma suka samu raunuka a harin da jiragen yaƙin suka kai sansanin gudun hijira na al-Mawasi.
Isra'ila ta kai wannan hari ne a jiya Asabar, an kai gawarwakin wasu daga Shahidan da masu raunuka asibitin Nasser Hospital dake Khan Younus.
Firaministan haramtacciyar ƙasar Isra'ila Benjamin Netanyahu bayyana cewa sun kai wannan hari ne domin kashe kwamandan rundunar Hamas mai suna Muhammad Deif.
Sai dai shi kan shi Netanyahu ya bayyana cewa basu da tabbacin ko sun kashe Deif ko basu kashe shi ba kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Aljazeera ta labarto.
Mataimakin shugaban Hamas na zirin Gaza Khalil al-Hayya ya bayyana cewa wannan iƙirarin na Netanyahu cewa sun hari Deif ƙarya ne.
Wani shaidar gani da ido ya bayyana ma kafar yaɗa labarai ta BBC cewa harin ya faru kamar girgizar ƙasa, ƙasa ta girgiza gini ya rushe ya danne mutane, haka jami'an agaji suka yi ta zaƙulo mutane daga baraguzan gini.
Israel bombed refugee tents in the very Muwasi area they designated as Gaza’s sole “safe zone”, then bombed fire fighters that came to the rescue.
— Muhammad Shehada (@muhammadshehad2) July 13, 2024
A carnage of epic proportions, with about 50-100 people murdered! pic.twitter.com/6CRHwvPukx
Wannan sansani na al-Mawasi Isra'ila ce da kanta ta sa Falasɗinawa suka tare a wurin tun cikin watan October kwanaki kadan bayan fara yaƙin, saboda tace nan "Safe Zone" ne, amma Isra'ila ta kai hari sansanin lokuta mabanbanta
Ko a cikin watan June da ya gabata sojin Isra'ila sun kai hari sansanin sun kashe Falasɗinawa 22 a Ofishin hukumar agaji ta "International Committee Of Red Crescent dake al-Mawasi wanda ɗaruruwan Falasɗinawa ke zaune a wajen.
Bayan faruwar lamarin kasashen yankin na gabas ta tsakiya Iran,Turkiyya,Qatar,Haɗaɗɗiyar daular Larabawa ta Dubai, da Saudi Arabia duk sun yi Allah wadai da wannan hari kuma sun jaddada kiran a tsagaita wuta.
Bayan wannan mummunan harin Isra'ila ta sake kai wani kazamin hari yayinda wasu Falasɗinawa suke sallah a kusa da wani masallaci a sansanin gudun hijira na Shati Refugee Camp dake Gaza, wannan harin ya kashe Falasɗinawa 20.
Daga fara yaƙin nan zuwa yau dai Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 38,000 mafi yawancin su Mata ne da Yara.
0 Comments