Sojin Isra'ila Sun Kashe Mata Da Ƴarta Da Wasu Kwamandojin Ƴan Muqawama Biyu Da Abokin Aikin Su Ɗaya.



Daga - Mahadi Tukur Almizan

Sojin Isra'ila sun kashe wata mata da ƴarta a wani hari da suka kai Tulkarem


Sojin na Isra'ila sun kashe matar mai suna Iman Abdullah Salem mai Kimanin shekaru 56 da ɗiyar ta ƙarama a wani hari da sojin na Isra'ila suka kai birnin Tulkarem dake yammacin gabar kogin Jordan a jiya Talata 23 July.



Hakanan a jiya Talata ɗin ne wani jirgin sojin Isra'ila mara matuƙi ya kai hari ya kashe wasu mayaƙan rundunar Hamas da rundunar Al-Aqsa Matyrs Brigade su uku.


Biyu daga cikin mayaƙan na rundunonin ƴan muqawama daga cikin uku da harin na Isra'ila ya kashe kwamandoji ne, sai kuma ƙaramin mayaƙi ɗaya


 


A jiya Talata rundunar Al-Aqsa Matyrs Brigade ta sanar da cewa Isra'ila ta shahadantar da Kwamandan ta a Tulkarem Mohammed Awad da Mohammed Ibrahim Badie.


A sanarwar ta su sun jajanta ma rundunar Qassam Brigades bisa shahadar ɗaya daga kwamandojin rundunar mai suna Ashraf Eid Zaher Nafe.


"Mayaƙan uku sun yi shahada ne a yayin da suke aikin bada kariya a sansanin gudun hijira a Tulkarem sakamakon wani hari da Isra'ila takai" cewar rundunar ta Al-Aqsa Matyrs Brigade.

Zaku iya kallon yadda harin ya faru a cikin bidiyon dake ƙasa

Sai dai kafar yaɗa labarai ta WAFA News Agency ta bayyana cewa sojin na Isra'ila sun kwashe gawarwakin shahidan.


Kafafen yaɗa labarai na Isra'ila sun saki bidiyon yadda jirgin maras matuƙi ya kashe mayaƙan ƴan muqawama su ukun.


Wannan harin ya biyo bayan musayar wuta tsakanin sojin na Isra'ila da mayaƙan gwagwarmaya daga rundunoni mabanbanta dake fuskantar sojin Isra'ila a Tulkarem tun bayan da sojin Isra'ila suka yi ma sansanin ƙawanya a yammacin ranar Litinin.



A lokacin da sojin na Isra'ila suka yi ma Tulkarem ƙawanya sun lalata abubuwan more rayuwa kamar yadda suka yi a West Bank.


Sun yi amfani da motocin rusau da ake kira 'Bulldozzer' sun rusa gidaje kuma ɓarnar su ta haddasa matsalar rashin ruwa da kuma Network ɗin Internet kamar yadda kafar yaɗa labarai ta WAFA News Agency ta labarto.

Post a Comment

0 Comments