TASIRIN IYALAN SAYYID AL-ZAKZAKY A CIKIN TAFIYAR HARKA ISLAMIYYAH

 


Mafi Kyawon Ta'abiri gajere da za a yi siffanta aikin da su Sayyid Ahmad Al-zakzaky suka yi a cikin Harka Islamiyyah shine:


Karkato Zukatan Samari zuwa rungumar Addini, runguma shamila kuma kamila.


Sun nuna yadda ya kamata saurayi Ɗan Harka Islamiyyah ya kasance a Fikirance da Dabi'ance da aikace.

Duk wanda ya san Sulukinsu da Uslubin rayuwarsu, zai baka tabbacin cewa lallai zaki jarumtarsa na nasuwa zuwa ga 'ya'yansa.


A cikin salon rayuwa irinta Amadu Ɗan Sidi, da Hamidu Jikan Taju da Mahmudu magajin Malam, babu wani abu wai shi tsoron mutuwa, ko Firgita domin karfin Maƙiyi, ko fashin aiki domin wahalarsa.


Abu ɗaya suke lalabe a kullum, shine ya zamo abun gaskiya ne, kuma ya zamo a kan lokacin aiwatarda shi yake. Idan biyun nan suka haɗu to shi kenan zance ya ƙare, babu wani shinge ko wani tudu ko kwazazzabe, ko wata ƙaya ko wani Ƙarfi da ya isa yasa su ja baya daga aikata shi. Da suka yi imani da Allah, imani na Haƙiƙa, sai Allah ya masu muwafaqa da samun istiqama.


Tsoron mutuwa shine ciwon da ke sa mutum ya dawwama a Ƙasa, ya kasa cillawa Sama, zuwa Duniyar malakuti, komai Iliminsa, komai ibadarsa, matukar akwai tsoron mutuwa a tattare da shi(tsoron mutuwa ba na Al'ada ba), to zai dawwama yana hidima ne ga wannan Duniyar. Burin yin haduwa da Allah shine alamar nuna da gaske ake wajen bin Allah.

Al-Qur'an ya ce: "To ku yi Burin mutuwa mana idan kun kasance masu gaskiya".


Kenan alamar bin Allah da gaske shine rashin tsoron bada rai a Tafarkin Allah. Wannan shi zai hana mutum ya ji tsoron wani Ƙarfi wanda ba na Allah ba.


To a gidan Ali Tajo, babu tsoron Tinƙahon Duniya, babu Tsoron Amurka, babu tsoron Ingila, babu tsoron Faransa, balle wasu karnuka nasu can gefe. Tsoron Allah kawai suka sani. Sai gaskiyarsu ta zamo lamba ta Ɗaya.


Ana iya finsu ilimi na takadda, ko yawan surutu a sifika ko a jarida ko talabijin, amma ba a fisu gaskata sakon Allah ba. Ana iya finsu sanin Ilimomi amma ba a fisu Tazkiya ba. Shiko ilimi babu Tazkiya Azaba ne. Ana iya finsu shekaru, amma ba a fisu Sallamawa Allah ba. Minene Amfanin shekaru a cikin shakku da rudu? Ta nan suka sha gaban kowa, suka shalle kowa, bisa turmuzar hancin Magauta. Aikinsu a July 2014 sheda ne a kan haka.


Dama kafin nan a haka suke, ga ƙarfin Imani ga Kaifin basira, Sannan ga wata kalar Natsuwa da tawali'u wadanda suka yi musu zayyana, suka kara masu haske.


Mutuwa a wajen Alu tajo sunanta Gada, wadda ta zo domin ta Sawwaqe hanyar haduwa da muradinsu, hanyar haduwa da mahaliccinsu. Shi yasa suka zaɓi tun yanzu su tafi, tun yanzu su samu shahada ba sai Imam ya bayyana ba.


 Hakan ya masu sauƙi ne saboda tun asali su Zuciyarsu Sama take hankoron ba Ƙasa ba. 


Mutuwa a wajen Magauta Alu tajo, ba komai bace illa kulki wanda ke dukarsu yana korarsu daga Duniyar da itace Muradinsu itace abar nemansu. Saboda tun asali su Ƙasa suke lalabe ba sama ba. Dasu da karnuka babu bambamci.


ولكنه أخلد إلى الأرض فمثله كمثل الكلب...



Rashin tsoron mutuwa a kan Tafarkin Allah, siface Dawwamamma a cikin jinin wannan ya gida mai Albarka. Hakama jinkan Raunana.


Don haka kyakkyawan koyi ya tabbata a garemu a cikin Sulukin iyalan gidan Sayyid Ibraheem Al-zakzaky.


Shamsudeen Hassan Zuru

Post a Comment

0 Comments