TASIRIN IYALAN SAYYID AL-ZAKZAKY A CIKIN TAFIYAR HARKA ISLAMIYYAH (3): SIRRIN SHAHADARSU A RANAR QUDUS.

 


Sun miƙa rayuwarsu, da su da sauran Shahidai, domin goben sauran mutane ta yi kyau, ‘Yanci da Aminci su tabbata a doron Ƙasa, domin ci gaba da bunƙasa su zamo makoma ta karshe ga wannan Nahiyar, wadda ta yi asarar duk wani abu da ake kira ci gaba.

Yadda Zuciyarsu take cike da fata na gari, haka Shahadarsu ta zo ta cusa kyakkyawa fata da zabura a cikin Ruhin miliyoyin Matasa.
Yadda suka gina Shahksiyyarsu da Imani da Makarimul Akhlaq dayawan ibadoji, haka Shahadarsu ta yi tasirin sauya Zukatan kasalallu ta mayarda su jajirtattu, Gwaraza Mazajen fama.

Yadda suka dake a gaban Karnuka da Birai, suka nuna masu su Zakokin Dawa ne, haka tafiyarsu ta mayarda miliyoyin Samari dakakku jajirtattu, waɗanda suka girgiza ƙasa a Abuja da Kaduna da kewaye, suka razana Hantar Magauta.

Basu juya ba, basu bada baya ba, sun tunkari mutuwa suka razanata, domin sun san juyawa a gaban Maƙiyi Ƙasƙanci ne ga mumini. Balle a ce Maƙiyin Basahayune ne ko Ba’amurike ko karnukansu,waɗanda babu abunda suke so irin a ji tsoronsu, babu abunda suka tsana irin a ɗaukesu banzaye, domin daman Banzayen ne kuma Birai..

A rana Qudus ta 15 July ɗin 2014 ne Iyalan gidan Sayyid Ibraheem Al-zakzaky suka ɗauki nauyin canza balance na karfin Sahayunawa a wannan Nahiyar tamu. Tun daga ranar a kullum girmansu raguwa yake, kaka gidansu sai ƙasa yake, mutane sai farkawa suke. Su kuma su Sayyid Ahmad, Hamid da Mahmud haskensu sai dada shiga Zukata yake.

Akwai Sirri mai dimbin yawa da ya zamo Shahadarsu ta faɗo a ranar Qudus ne, ba ranar wata munasabar ba..

Kaɗan daga ciki shine, ta yiwa ruɓaɓɓun Shi’ah a wannan Nahiyar, masu jiran su yi hijacking din Harka Islamiyyah kwalelenku. Domin jininsu ya zamo mai dakon matsalar Falasdinu a cikin Jijiyoyin Harka Islamiyyah, har gaba da abada. Gwagwarmayar Kwatar yanci babu fashi kenan. Jininsu yayi yamma da yan kwamashiyal na cikin gida da waje.

Jininsu ya ɗaure manufofin Harka Islamiyyah a tsakiyar Zukatan Samari sabbin jini masu tasowa, wanda wannan guarantee ne na cewa baya za ta yi kyau.

Zubar jininsu a ranar Qudus, ya gajiyarda hukumomin zalunci cimma burinsu a kanmu, na mantawatda matsalar Falasdinu a wannan Nahiyar.

Haka da jininsu ne Sahayunawa suka zamar mana Maƙiya mubasharatan ta yadda a nan gaba sun zamar mana legitimate target, domin Har yanzu akwai equation a tsakaninmu da za mu yi settling. Da jininsu ne wannan nahiyar za ta kubuta daga kaka gidan Amrkawa da Sahayunawa a nan gaba ta kusa Insha Allah.

Albarkar zubar wannan jini a ranar Qudus saninta sai Allah mahaliccinsu. Ba accident bane, devine plan ne.

Jininsu ya buɗe sabon shafin Muwajaha, ya buɗe idanu ya tayarda Samari daga bacci. Ya saka masu fata, ya ƙara masu siƙa da Jagora, da siƙa da hanyar Jagora da siƙa da samun Nasara a kan hanyar da siƙa da cewa hanyar itace hanyar Annabawa da Imamai. Hanyar Istiqama, hanyar kin jin tsoron Maƙiya, hanyar Bara’a ga & Dawagitai hanyar Zakzakiyyanci a cikin Sulukin Ahmadiyyanci.

Mutum na iya tambaya yace, Shin su Sayyid Ahmad sun samu wannan Nasara ne kawai domin su ɗiyane ga Jagora?

Amsa ko kaɗan. Falkawa suka yi, wayewa suka yi, fahimtar manufa suka, korar jahilci suka yi, Imani suka yi, Jarumta suka yi, basira suka yi, Juriya suka yi, gane Hadafi da wasilar cimma Hadafi suka yi, sai suka zamo role model Ga MASU Shauƙin yin yadda suka yi,da zamowa yadda suka zamo. Faqat bakin nan.

A nan muka tu ƙe,
A nan muka tsaya,
A nan muke fatan dawwama.

Shamsudeen Hassan Zuru
26/7/2024


Post a Comment

0 Comments