TASIRIN IYALAN SAYYID AL-ZAKZAKY A CIKIN TAFIYAR HARKA ISLAMIYYAH (4 Ƙarshe)

 



Natsuwar wasu tana ƙarƙashin samun kofin Shayi mai zafi tare da kayan maƙulashi a cikin parlor mai ɗumi, a lokacin sanyi ko Damina.

Wasu kuma Natsuwarsu na cikin fizgar cinyar Kaza ko balangu mai kanshin yaji wanda ya ji magi da citta a ƙarƙashin bishiya kusa da Rafi
Wasu kuma tasu Natsuwar na ƙarƙashin dafe Dubban miliyoyi, ko gina katafaren gida, da auren manyan mata. Wasu kuma Natsuwarsu itace lalaben Mukami da babbar kujera a fagen siyasa dana kasuwa da Addini.

Duk wannan tarkacen baya gaban Iyalan Tajo. Su Natsuwarsu tana ƙarƙashin komawa gidan dawwama jikkarsu cike da tarin Yardar Allah.
Shi yasa a kullum tunanunsu da aikinsu yana a kan Addini ne. Takensu shine taimakon raunana, kirarinsu kuma yakar zalunci, tambarinsu Bara’a, zagensu Wilayah.

Sallamawarsu ga Allah ta saka Zuciyarsu ta zamo mai saurin karɓar irshadin Al-Qur’ani da koyarwar Ma’asumai. Sai Zuciyarsu ta tsarkaka tun daga tushe har Reshe.

Sarkin zuciya ake so, ba tarin shekaru ko tarin kuɗi ko mukamai ba, kai hatta tarin Ilimi shirme ne idan babu tsarki zuciya.

و يزكيهم و يعلمهم الكتاب و الحكمة.

Sun samu tsarkinta zuciya tun suna Samari. Sai Allah ya sanarda su Sirrin littafi, dama Hikima Gadonsu ce.

Da suka Miƙawa Allah komai nasu, sai Allah ya hore masu hanyar hanyar komawa zuwa gareshi da Sanyin maice, malaikun Rahama suka shimfida fikafikan ƙudura suka masu iso a babbar fada. Suna faɗin :

Ya ku wadannan rayuka natsattsu, ku koma zuwa ga ubanjinku kuna yardaddu abuben yarda.

Mu kuma muna faɗin :

Wa Sayyidi Ahmad waah Mahamuuud..
Wa Sayyidi Hamid waa Shuhadaaah.. 😢
Ina ‘Yan Uwa mabiya Zakzaky..

Kuna ina an kashe dansa haziƙi.
Shin baku so ku bada rai ga Zakzaky.
Kun fi son Yahudu suita mana tarnaƙi.

Sallama ga Amadii
Wilayah ga Zakzaky
Gaisuwa ga Mahadi.

Shamsudeen Hassan Zuru


Post a Comment

0 Comments