Daga - Almujtaba Abubakar
A wannan ranar bayan mun idar da Magrib da Isha'i, Jagora(H) ya fito domin gabatar da Buɗa baki kamar yadda aka saba.
Jagora Syed Zakzaky(H) ya fara da cin Dabino, ya ɗauki ruwan shayi ya sha kaɗan, sai ya ɗaga kansa sama, ya ɗan yi shiru... Sai ya fara bayanin yadda aka harbi Muhamud, a lokacin labarin Shahada su Syed Ahmad bai iso ba.
Cen sai ga wasu 'Yan uwan Abba(H) ( Dattijan Mata) sun shigo gidan, suna zuwa inda su Jagora ke zaune sai suka rungume shi suna kuka, kuka sosai, a lokacin akwai wani daga cikin 'Yan uwan su Jagora (H) dake wurin,sai ya mike da nufin ya ɗaga Matan daga jikin Abba, sai Abba(H) ya yi masa ishara da hannu ya ce ya kyalesu, daga baya Dattijan Matan da kansu suka tashi suka shiga cikin Gida zuwa sashen Umma (mahaifiyar Jagora).
A daidai wannan lokaci ne sai ga su Malama Maimuna Matar Sheikh Turi ta shigo gida, ta tsuguna da nufin yi wa su Abba (H) jaje, sai aka kira Jagora a waya, bayan ya ɗaga sai mu ka ji kururuwar tashin sautin Kuka me karfi ya sake tashi daga cikin Gida, sai kuma mu ka ji Jagiora (H) na faɗin "INNALILLAHI WA INNA ILAHI RAJI'UN", ya na ta faɗin haka ya na maimaitawa har sau uku.
Bayan Jagora(H) ya aje wayar, sai ya sunkuyar da Kai kasa, cikin gaggawa Sheikh Turi ya tambayi su Abba me ke faruwa, buɗar bakin su Abba(H) sai ya ce an kashe su Ahmad, INNALILLAHI WA INNA ILAHI RAJI'UN... Dajin haka sai Malama Maimuna matar Sheikh Turi ta faɗi ta Suma a wurin, mu kuma kowa ya fashe da Kuka, wasu na dukan ƙasa, wasu na dukan bango, (alamun baƙin ciki.
Sai Jagora ya mike ya shiga cikin Gida, jim kaɗan ya sake fitowa ya ce, an kira shi an faɗa masa cewa sojojin sun motar 'Yan ISMA da aka tura domin karɓo gawar su Ahmad, daman su Shahid Dakta Mustapha ne a ka tura karɓo gawar, sai daaga baya ne aka sake su.
Bayan na fito wajen Gidan, sai na ga Muhammad Maina (Ayatullahi), zaune a gefen Hanyar Ruwa tareda Shaheed Abdullahi (Sufi), Muhammad na kuka, ya na rerwa wasu baitulan waken bakin ciki da larabci, hawaye na kwarara, na kalli Muhammad Ayatullahi, sai na ji hawaye ya sake kwararowa a Idona.
Na ga tanshin Hankali a wannan daren, na ta shi na koma gida, da yake gidanmu bai da nisa da Gidan Jagora(H), na faɗawa mahaifana abin da ke faruwa.
Na ɗauki kusan watanni ina ganin kamar su Ahmada su na nan a raye a cikinmu, kullum idan na je gidan Abba na kan yi tsammanin zan gansu a inda suke zama idan Sallah ko buɗa baki, sai dai ya zama ina yawan ganinsu a famarki idan barci.
Tausayin Jagora Allama Syed Zakzaky(H) ya ninku a zuciyata, na ɗauki lokaci, duk lokacin na tuna wannan ranar sai na hawaye na zuba a idona.
Allah ka kara hasken Rahama da kamshi a ruhin waɗanan Shahidan
0 Comments