A Safiyar Jiya Asabar Isra'ila Ta Hari Palasɗinawa Yayin Da Suke Sallar Asuba Mutum 100 Suka Yi Shahada



Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Wannan sabon harin ta'addancin na Isra'ila ya zo ne daidai lokacin da Amurka ta bada damar turo zunzurutun kuɗi har dalar Amurka $3.5 biliyan domin Isra'ila ya siya makamai.


Sojin Isra'ila sun ƙaddamar da sabon harin ta'addanci da safiyar jiya Asabar 10 ga watan August, harin ya tarwatsa kafatanin makarantar Al-Tabiin da Palasɗinawa suke gudun hijira a ciki dake al-Daraj wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutum 100 sannan kuma ya raunata wani adadi mai yawa.


hukumar Civil Defense ta Gaza ta bayyana cewa "An samu shahidai aƙalla 100 da kuma masu raunuka da yawa sakamakon jefa bom da Isra'ila ta yi a makarantar da ake gudun hijira a ciki a kusa da al-Daraj dake gabashin birnin Gaza".


"Sojin mamaya sun hari sansanin gudun hijirar da missiles guda uku a lokacin da suke yin sallar Asuba a makarantar ta Al-Tabiin school " duk a cikin bayanin na hukumar Civil Defense ɗin ta Gaza



Sun fara sallar Asuba da misalin ƙarfe 4:37 rahoto ya nuna cewa Isra'ila ta jefa missiles ɗin da misalin ƙarfe 4:44 ƴan mintuna kaɗan bayan fara sallar.


Shugaban hukumar bada agaji a kudancin Gaza ya bayyana ma kafar yaɗa labarai ta Aljazeera cewa "Duk yadda zan yi ƙoƙarin bayyana wannan ta'addancin, bazan iya bayyana haƙiƙanin sa ba".


Ya kara da cewa lokacin da ya iso wurin da lamarin ya faru sun iske mutane sun yi filla filla sassan jikin wani kan wani, maza da mata da ƙananan yara duk sun yi filla filla sun ƙone ƙurmus".


" Dole ne duniya ta ɗauki matakin dakatar da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi kan al'ummar Palasɗinu".


 


Isra'ila ta fitar da bayani inda ta nuna ta kai harin ne saboda jami'an Hamas suna ɓoyewa cikin fararen hula.

Post a Comment

0 Comments