Ƴan Muqawama Na Iraqi Sun Gargaɗi Cewa Za Su Fuskanci Hare Hare Babu Ƙaƙƙautawa Idan Suka Yi Amfani Da Sararin Saman Iraqi Wajen Kaima Iran Hari

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Yiwuwar ɓarkewar yaƙi tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran da ƴan muqawama nata ƙaruwa tun biyo bayan kashe Isma'il Haniyeh a birnin Tehran.


A jiya Litinin 12 ga watan Agusta kwamitin tsarawa na gamayyar ƴan muqawama na Iraqi da ake kira 'Iraqi Resistance Coordination Commitee' (IRCC) ya gargaɗi Amurka cewa martanin da za su mayar kan dakarun na Amurka ba ya da iyaka idan har suka amfani da sararin samaniyar Iraqi wajen kaima Iran hari, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Shafaq News ta labarto.


Kwamitin da ake kira IRCC yana wakiltar ƙungiyar ƴan muqawama ta Iraqi ne da ake kira 'Islamic Resistance in Iraq' wadda ta ƙunshi gamayyar kungiyoyin ƴan muqawama ƴan shi ma su adawa da ci gaba da zaman sojin Amurka a ƙasar ta Iraqi, wanda suka haɗa da Kata'ib Hezbollah,Asa'ib Ahlal Haq, Kata'ib Sayyidus - Shuhada, da kuma Harakat Hezbollah al-Nujaba, wasu daga cikin waɗannan rundunoni na ƴan muqawama suna daga cikin gamayyar dakarun tsaron Iraqi da aka fi sani da 'Quwwatu Hashad Assha'abi' da turanci 'Popular Mobilization Units' (PMU).


Ko a cikin satin da ya gabata ƙungiyar ta IRI ta ɗauki alhakin wani hari da aka kai sansanin sojin Amurka da ake kira Ain Al-asad dake gundumar Anbar wanda ya raunata Amurkawa 5.


A ranar 31 ga watan July ne sojin Amurka suka hari wani sansanin dakarun Kata'ib Hezbollah dake Iraqi wanda ya yi sanadiyyar shahadar wani babban ɗan kasar Yemen masanin missiles mai suna Hussein Abdullah Mastour al-Shabal, kuma a wannan ranar ne Isra'ila ta kashe Isma'il Haniyeh a birnin Tehran na ƙasar Iran, hakanan kwana ɗaya kafin nan  Isra'ilar ta kashe kwamandan Hezbollah Fu'ad Shukr a birnin Beirut na kasar Lebanon.


Iran da Hezbollah sun yi alƙawarin mayar da martanin wannan kisa, a gefe guda kuma Amurka ta yi alƙawarin baiwa Isra'ila kariya koda yaƙi zai barke tsakanin Iran da Isra'ilar.


Kwamitin na IRCC ya bayyana cewa "Duk da munanan hare haren da ke sauka kan ƴan uwan mu, amma dakarun Amurka sun fifita baiwa sahayuniyawa kariya sama da zaman lafiyan yankin gabas ta tsakiya, suna keta hurumin ƙasar Iraqi su da kansu suna karya dokokin da suka ƙirƙira".


"Dan haka idan har Amurka ta sake ta hari mutanen mu a Iraqi ko tayi amfani da sararin samaniyar Iraqi wajen kai ma Iran hari to zata fuskanci hare hare da basu da linzami".


Sai dai wata majiya ta faɗi ma kafar yaɗa labarai ta Shafaq News cewa sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya gargaɗi firaministan Iraqi Muhammad Shi'a al- Sudani akan ƴan muqawama da ya kira ƴan koren Iran cewa suna kokarin faɗaɗa yaƙi da sojin Amurka a Iraqi da ma yankin gabas ta tsakiya.


Shima al- Sudani a nashi bangaren ya nemi Amurka su tabbat sun kiyaye harar dakarun PMU da dukkanin bangarorin su, domin hakan ne zai sa bangarorin biyu su dakata.

Post a Comment

0 Comments