Daga - Mahadi Tukur Almizan
Binciken sababin mutuwa da ake yi ma gawa domin sanin abinda ya yi sanadiyyar mutuwa da ake kira Autopsy ya nuna kaso mafi yawa daga cikin Palasɗinawan da suka yi shahada a wuraren da Isra'ila ke tsare dasu ansamu gawarwakin su da karyayyun haƙarƙari wannan ya nuna tsananin azabar da ake yi masu ce ta yi sanadiyyar shahadar su.
Wani rahoto da sojin Isra'ila suka baiwa wata kungiyar kare haƙƙin ɗan Adam da suka nemi rahoto daga hannun sojin na Isra'ila ya nuna cewa daga 07 October zuwa 2 July Palasɗinawa 44 suka yi shahada daga cikin waɗanda suke tsare a hannun sojin Isra'ila.
Ƙungiyar da ta nemi rahoton daga hannun sojin na Isra'ila ita ce 'Physicians for Human Rights Israel ' kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Almayadeen ta bayyana.
Bayan fitar wancan rahoton kamfanin dillancin labarai na 'The Wall Street Journal' ya gudanar da bincike kan sahihancin rahoton da sojin Isra'ila suka bayar, sai dai wannan bincike na su ya sake bankaɗo karin shahidai 16 da suka rasa rayukansu a gidajen yarin Isra'ila, su waɗannan a gidajen yarin ne suka yi shahada ba a hannun sojin ba, sai dai haryanzu hukumomin Isra'ila sun ƙi sakin rahoton Autopsy na wadannan shahidai.
Sai dai ire iren wadannan rahotanni da Palasɗinawan da ke yin shahada a hannun sojin na Isra'ila bai zama abun mamaki ba tunda ɗaya daga cikin ministocin Isra'ila Ben Gvir ya kira yi hukumomin Isra'ila da su riƙa kashe Palasɗinawan da suke tsare da su.
Itamar Ben Gvir dai shine ministan ƴan sandan Isra'ila kuma shine mai kula da tsarin gudanarwar gidajen yarin Isra'ila, a cikin watan June ya yi kira da a kara tsaurara ma Palasɗinawan da ake tsare da su, ciki har da neman a rage masu abinci.
Hakanan a cikin watan April ya nemi a zartar da hukuncin kisa kan wasu daga cikin tsararrun na Palasɗinawa domin a rage cinkoson da ke da akwai a gidajen yarin na Isra'ila.
Tun daga 7 ga watan Oktoba na shekarar 2023 sojin Isra'ila sun kama dubun nan Palasɗinawa daga Gaza da West Bank Wanda ya sa adadin Palasɗinawan da Isra'ila ke tsare da su yakai 9,000 wannan alkaluman da hukumar gidajen yarin Isra'ila ta baiwa wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta Isra'ila da ake kira 'Hamoke' ne.
Wata takarda da shugaban hukumar tsaron Isra'ila ta cikin gida da ake kira 'Shin Bet' ya saka ma hannun a watan karshen watan June ta gargaɗi cewa yanayin da tsararrun Palasɗinawa suke ciki ya saɓa da dokokin majalisar dinkin duniya dan haka takardar ta nemi a karfafa baiwa jami'an hukumar Red Cross damar kulawa da tsararrun Palasɗinawan sannan kuma a ƙalubalanci masu azabtar da su a gidajen yarin.
0 Comments