Daga - Muhammad Attahiru
Ƙungiyar gwagwarmayar ƴanto Falasɗinu wato Hamas ta sake jaddada cewa, duk wata yarjejeniya da zata yi da Isra'ila dole ne ta tabbatar da tsagaita buɗe wuta a Gaza da kuma janyewar sojojinta gaba ɗaya tare da amincewa da musayar fursunoni.
Ƙungiyar gwagwarmayar ta Falasɗinu a cikin wata sanarwa da ta fitar a shekaran-jiya Alhamis ta ce, kamata ya yi yarjejeniyar ta sauƙaƙa wajen dawo da Falasɗinawa da suka rasa matsugunansu da kuma sake gina yankunan da aka lalata.
"Hamas na kallon tattaunawar da ake yi a Doha dangane da tsagaita buɗe wuta da musayar fursunoni daga mahangar dabaru da nufin kawo ƙarshen ta'addanci a Gaza," in ji wani jami'in Hamas Hossam Badran a cikin sanarwar.
Badran ya ƙara da cewa, "Hamas ta yi imanin cewa, duk wata tattaunawa dole ne ta kasance bisa wani tsari mai tsauri don aiwatar da abin da aka amince da shi a baya. Abin da ke hana cimma yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a Gaza shi ne ci gaba da gujewan Isra'ila."
"Duk wata yarjejeniya dole ne a cimma cikakkiyar tsagaita bude wuta, da ficewa (Isra'ila) gaba ɗaya daga Gaza, (da) dawo da ƴan gudun hijira, tare da yarjejeniyar musayar fursunoni," in ji Hossam Badran.
Sanarwar ta Hamas ta jaddada cewa, dole ne duk wata tattaunawa ta kasance bisa wani tsayayyen tsari na aiwatar da yarjejeniyar da aka ƙulla, wadda aka amince da ita a farkon watan Yuli, kamar yadda kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da yarjejeniyar.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da wani sabon zagayen tattaunawar sulhu a Doha, inda Hamas ta zaɓi ƙin shiga. A maimakon haka, ƙungiyar ta buƙaci masu shiga tsakani da su aiwatar da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya maimakon yin ƙarin tattaunawa kan wata sabuwa.
Hamas ta sha bayyana shirin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta, amma ta ce ci gaba da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza ya tabbatar da cewa gwamnatin ba da gaske take ba game da tsagaita buɗe wuta na dindindin.
Ɗaya daga cikin jami'in Hamas Ahmad Abdul Hadi ya faɗa a ranar Laraba cewa "(Hamas) ba za ta shiga sabuwar tattaunawa da gwamnatin Isra'ila kan tsagaita wuta a Gaza ba."
Baya ga Hadi, babban jami'in Hamas Sami Abu Zuhri shi ma ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a wannan rana cewa, Hamas ta jajirce kan shawarar da aka gabatar mata a ranar 2 ga watan Yuli, wanda ya dogara da ƙudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da jawabin Biden da yunƙurin.
"An shirya fara tattaunawa kan hanyar aiwatar da shi wannan yunƙurin nan da nan" in ji Zuhri. Ya kuma ci gaba da cewa, "za a fara tattaunawa kan sabbin shawarwarin."
An bayar da rahoton cewa Isra'ila ta gabatar da sabbin buƙatu a tattaunawar tsagaita wuta bayan Hamas ta amince da sabbin sharuddan.
A halin da ake ciki dai gwamnatin haramtacciyar ƙasar Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare ta sama da ta ƙasa a yankin Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya a daidai lokacin da ake shiga wata na goma sha ɗaya da fara yakin kisan kare dangi.
Kisan gillar da haramtacciyar ƙasar Isra'ila ta aiwatar na baya-bayan nan a Gaza ya sa adadin Falasɗinawa da aka kashe kaiwa mutum 40,000 tare da jikkata wasu fiye da 92,400.
Freedom Fighters Ng
0 Comments