Daga - Mahadi Tukur Almizan / Abdurrahman Bala Idris
Dakarun Amurka a Iraki da Syriya sun fuskanci hare-hare a ƴan makonnin da suka gabata sakamakon ƴan muqawama na cikin gida sun dawo kai hare haren goyon bayan Falasdinu
Aƙalla sojojin Amurka biyar da wasu ƴan kwangila suka jikkata sakamakon wani harin roka da aka kai kan sansanin sojin saman Amurka da ake kira Ain al-Asad da ke Iraqi a ranar 5 ga watan Agusta, kamar yadda jami’an fadar tsaron Amurka 'Pentagon' suka tabbatar.
Jami'an tsaron Amurka sun bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa a kalla mutum daya ya samu "mummunan rauni." Jami'an da ba a bayyana sunayensu ba sun kara da cewa:
"Ma'aikatan sansanin suna gudanar da bincike kan barnar da harin ya haifar."
Sojojin Amurka sun karbe iko da Ain al-Assad a shekara ta 2003 bayan mamayar da fadar White House ta yi ba bisa ka'ida ba tare da mamaye kasar amma sun janye sojojinsu a shekarar 2011 lokacin da Barack Obama ya kasa cimma sabuwar yarjejeniyar Sojojin (SOFA) a tsakanin shi da firaministan Iraki na wancan lokacin Nouri al - Maliki.
Sai dai sojojin Amurka sun sake dawowa sansanin na Ain Al-asad da nufin horas da ƴan kasar Iraqi don yaƙar ISIS, bayan yan ta'addan ƙungiyar ISIS sun mamaye birnin Mosul da watanni shida, birni na biyu mafi girma a Iraqi a watan Yunin 2014.
Tun wancan lokacin sojin na Amurka ke zaune a sansanin sojin na Ain Al-asad zuwa yau.
An kai hari akalla sau biyu a sansanin sojin saman na Ain al-asad a cikin makonni uku da suka gabata yayin da kungiyoyin gwagwarmaya na cikin gida da ke aiki a karkashin inuwar kungiyar Islamic Resistance in Iraq (IRI) ke ci gaba da gudanar da hare haren goyon bayan Palasɗinu da suka dakatar a farkon wannan shekarar.
Harin na ranar Laraba ya zo ne ƴan kwanaki kadan bayan wani harin da Amurka ta kai ya kashe mambobin kungiyar yaki da ta'addanci Popular Mobilisation Units (PMU) a arewacin Babil.
"Duk da kokarin da hukumomi ke yi na hanyoyin siyasa da diflomasiyya don kawo karshen cigaba da zama a ƙasar ta Iraqi da sunan yaƙar ƴan ISIS.
Mai magana da yawun firaministan Iraqi a bangaren soji Major Janar Yahya Rasool ya bayyana cewa Amurka da Iraqi za su samu kyakkyawar alaƙa da fahimtar juna ne idan aka girmama kuma aka kare hurumin iyakokin ƙasar ta Iraqi, amma sojin na Amurka suna ɓata wannan yunkurin ta hanyar kai hare hare a cikin ƙasar.
0 Comments