Firaministan Bangaladesh, Hasina Ta Yi Murabus Ta Gudu Zuwa Indiya.

 


Daga - Muhammad Attahiru

Hasina, wadda ke jagorantar ƙasar tun daga shekara ta 2009 ta hau jirgi zuwa ƙasar Indiya domin neman mafaka.


Ajiye mulkin Hasina ya zo ne bayan dubban masu zanga-zanga sun fantsama kan titunan ƙasar suna neman ta sauka daga muƙaminta.


Kwana ɗaya kafin ajiye mulkin Hasina, an samu mummunan gwabzawa tsakanin masu zanga-zanga da ƴansanda, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 90.


Masu zanga-zanga sun afka cikin gidan firaiministar da ke Dhaka, wato babban birnin ƙasar.


Kimanin mutum 300 ne aka kashe a ƙasar ta Bangaladesh bayan kwashe wata ɗaya ana zanga-zangar adawa da gwamnatin ƙasar.


A watan da ya gabata ne dai ɗalibai suka fara wata zanga-zangar lumana suna neman gwamnati ta yi watsi da tsarin raba-daidai na ayyukan gwamnati, sai dai tun daga wancan lokacin lamarin ya ƙazance zuwa adawa da gwamnatin ƙasar baki ɗaya.


Daga nan ne masu zanga-zangar suka koma kiraye-kirayen saukar firaiministar daga kan muƙaminta.


Firaiminista Hasina ita ce shugaban ƙasar da ta kafa Bangladesh kuma ita ce macen da ta fi kowacce dadewa a kan mulki a duniya.


A shekaru 15 da ta shafe a kan mulki, akwai zargi mai karfi na cewa mutane na bacewa kuma ana gallaza wa masu adawa. Zarge-zargen da Hasina ta musanta.


A cikin ƴan makonnin nan, Hasina da jam'iyyarta ta mai suna Awami sun zargi ƴan adawa da jawo rikici a kasar.


An kiyasta cewa dubun dubatar jama'a ne suka shiga zanga-zangar ba ɗalibai kawai ba. Wannan kuma shi ne kalubale mafi girma da ta fuskanta tun bayan sake zabenta a yanayi me cike da cece-kuce a watan Janairu.


Hasina ta soke tsarin guraben aiki inda hakan ya janyo bore tun daga farkon watan Yuli. Hakan yasa ɗalibai suka ci gaba da zanga-zanga suna kira ta sauka daga kujerarta.


Daga ƙarshe dai an hangi al'ummar ƙasar na wasoson ɗibar ganima a fadar gwamnatin na Hasina, yayin da aka hangi wasu ƙwance bisa gadon Firaiministar a matsayin nasu ganimar.


Freedom Fighters Hausa Ng🎙️

Post a Comment

0 Comments