Harin jirgin saman Isra'ila ya kashe Khalil Al-Maqdah a Lebanon.
Daga - Mahadi Tukur Almizan
Kisan na Khalil ya zo ne ƴan awoyi bayan rundunar Hezbollah ta zazzaga ruwan wuta a tuddan Golan (Golan Heights) da Isra'ila ta mamaye, Hezbollah ta mayar da martani ne kan harin da Isra'ila ta kai yankin Bekaa.
Khalil Al-Maqdah jami'i ne a tsagin soji na jam'iyyar 'Fatah Party' ta Palasɗinawa wadda ake kira 'Al-Aqsa Matyrs Brigades'.
An kashe shi ne a ranar Laraba 21 ga watan Agusta da muke ciki, a wani hari da jirgi maras matuƙi na Isra'ila ya kai kudancin Lebanon a birnin Saida.
The Israeli drone attack on a vehicle in Saida in the southern Lebanese depth killed one of the leaders of the Al-Aqsa Martyrs Brigades in Lebanon Khalil Al-Maqdah. pic.twitter.com/IYMlWjAwjE
— The Cradle (@TheCradleMedia) August 21, 2024
A cewar hukumar yaɗa labarai ta ƙasar Lebanon 'Lebanon's National News Agency' ta bayyana cewa "Jirgi maras matuƙi na Isra'ila ya hari abun hawa mai ƙafa huɗu a unguwar Villas dake birnin Saida kusa da masallacin Imam Ali, bayan faruwar lamarin jami'an Civil Defense da gungun wasu jami'an tsaro sun garzaya da motocin Ambulance zuwa wurin ba tare da ɓata lokaci ba, an hangi hayaƙi ya turnuƙe sama ya lulluɓe sararin samaniyar yankin".
"Wanda aka kashe ɗin shine Khalil Al-Maqdah, birgediya janar ne a kungiyar ta Fatah Movement, kuma yana aiki a bangaren soji na ƙungiyar" kamar yadda ɗan uwan shi mai suna Munir Al-Maqdah wanda shine Kwamandan rundunar ta Al-aqsa Matyrs Brigades ya bayyana ma kafar yaɗa labarai ta Almayadeen a ranar ta Laraba.
Munir ya kara da cewa "Kisa yana ƙara mana ƙarfi ne, wannan shahadar wani baje ne na girmamawa, kuma muqawama tana nan daram ta kama ƙasa".
Sai dai a wata sanarwa da sojin Isra'ila ta fitar sun bayyana cewa sun kashe wani ɗan ta'adda mai suna Khalil Hussein Al-Maqdah a garin Sidon dake kudancin Lebanon, kuma sun bayyana cewa Khalil ɗan uwan Munir Al-Maqdah ne wanda yake zaune a Lebanon yana aiki da kungiyar Hezbollah.
Sojin na Isra'ila sun kara da cewa wai a watan March na shekarar da muke ciki Khalil sa Munir sun shigo da makamai zuwa Judea da Samaria sun raba ma ƙungiyoyin ƴan ta'adda da suka baiwa horo a cewar sojin na Isra'ila.
Al-Aqsa Matyrs Brigades na daga cikin manyan rundunonin ƴan muqawama dake gumurzu da sojin Isra'ila a Zirin Gaza, hakanan akwai dakarun rundunar a West Bank.
0 Comments