Daga - Mahadi Tukur Almizan
Wani mummunan harin da Isra'ila ta kai ta sama a sansanin gudun hijira a Gaza ya yi sanadiyyar shahadar wani ahali abinda da turanci ake kira Family.
Harin ya faru ne a sansanin gudun hijira na Nuseirat Camp a ranar Talata wanda ya share gaba daya ahalin Abu Naba kamar yadda wata kafar yaɗa labarai ta Palasɗinawa ta labarto
Harin ya kashe iyalan gidan su bakwai, ciki harda Baba da Uwa da ƴaƴan su biyar masu shekaru tsakanin 2 zuwa 11.
Rahotanni sun bayyana cewa an ɗauki gawarwakin su zuwa asibitin shahidai ta "Al-aqsa Matyrs Hospital" dake tsakiyar Gaza, shi kuwa karamin yaron gidan mai shekaru 2 an same shi babu kai ma ajikin gawarshi.
Hakanan a ranar g 10 ga watan August da muke ciki wani harin sojin na Isra'ila ya kashe wasu jarirai tagwaye tare da Mamar su da kakarsu a Deir al-Balah dake tsakiyar Gaza.
Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta bayyana cewa aƙalla jarirai 115 hare haren Isra'ila suka shahadantar daga fara wannan yaƙin ta'addancin a zirin Gaza.
"Jiragen Isra'ila na cigaba da jefa bomai bomai a zirin Gaza sun kashe Palasɗinawa 32 sun raunata 88 a ranar da ake cika kwanaki 313 da barkewar wannan yaƙi " cewar wakilin kafar yaɗa labarai ta Palasɗinawa mai suna 'Maan News Agency'.
Hakanan sojin ƙasan Isra'ila na ci gaba da kai hare hare ta kasa a gabashin Khan Yunis tsawon kwanaki bakwai a jere, sun zagaye tare da rusa gidaje a garin al-Qarara da Abasan.
Jiragen yaƙin Isra'ila sun wata gona a kusa da Khan Yunis Court Complex, inda suka tarwatsa wajen, sojin kasa kuma sun raunata wasu mutane biyu a unguwar Araba dake gabashin Rafah.
Hakanan an samu gawarwakin mutum biyar a Rafah yayin da sojin na Isra'ila suka rusa wasu gidaje a Tel Al-Sultan dake yammacin birnin.
Zuwa yanzu dai hare haren ta'addancin Isra'ila wanda Amurka ta ɗaure ma wurin zama ya yi sanadiyyar shahadar Palasɗinawa 40,000 da kuma 92,152 da suka samu raunuka sannan kuma wasu dubunnai na ƙarƙashin ƙasa an kasa ƙwaƙulosu.
0 Comments