Daga - Abdurraham Bala & Mahadi Tukur Almizan
Kusan kashi 24% cikin 100% na wadanda aka kashe a yankin Gaza matasa ne, kuma kashi 70 na wadanda suka jikkata mata da yara ne.
Kusan kashi biyu cikin dari na daukacin al'ummar Zirin-Gaza Isra'ila ta kashe a yakin da take yi na kisan kare dangi, a cewar alkaluman da Hukumar ƙididdiga ta Palasɗinu 'PCBS' ta fitar a ranar 11 ga watan Agusta.
Sanarwar da ofishin ya fitar ta bayyana cewa Isra'ila ta kashe Palasɗinawa sama da 39,000 a Gaza.
"Wannan ya ƙunshi kusan kashi 1.8% na yawan jama'ar yankin," cewar PCBS ɗin.
A cewar bayanan, kusan kashi 24% na waɗanda Isra'ila ta kashe a Gaza matasa ne.
Bayanin ya ci gaba da nuna cewa mutane 34 ne suka mutu sakamakon yunwar da ta addabi yankin baki daya, inda ta kara da cewa yara 3,500 na cikin hadarin mutuwa sakamakon rashin abinci mai gina jiki da kuma karancin abinci.
Kimanin kashi 70% cikin dari na wadanda suka jikkata a Gaza mata ne da yara, inji PCBS.
Rahoton ya kara da cewa mutane 10,000 sun bace sannan kuma mutane kusan miliyan biyu suka rasa matsugunansu.
Tsakanin 7 ga Oktoba zuwa karshen watan Yuni, Washington ta baiwa Isra'ila jimillar bama-bamai kusan 30,000 wadanda aka yi amfani da su a zirin na Gaza.
A makon da ya gabata, Amurka ta haska wani kunshin makamai na dala biliyan 3.5 ga Isra'ila.
Adadin wadanda suka mutu a Gaza ya kai 39,897, yayin da 91,152 suka samu raunuka, a cewar majiyoyin kiwon lafiya da kamfanin dillancin labarai na WAFA ya ruwaito a ranar 12 ga watan Agusta.
"Har yanzu ma'aikatan agajin gaggawa ba su iya kaiwa ga mutane da dama da suka jikkata da gawarwakin da suka makale a karkashin baraguzan gine-gine ko kuma a warwatse a kan tituna a yankin da yaki ya daidaita, yayin da sojojin mamaya na Isra'ila ke ci gaba da dakile zirga-zirgar motocin daukar marasa lafiya da jami'an tsaron farar hula," kamar yadda likitocin suka bayyana ma kafar yaɗa labarai ta WAFA. .
Mujallar lafiay ta 'Lancet Medical Journal ' ta ambato masana a farkon watan Yuli na cewa adadin wadanda suka mutu zai kai tsakanin 149,000 zuwa 598,000 na Palasdinawa idan an kawo karshen yakin nan take.
Mujallar lafiyar ta wallafa wata takarda ta bincike tsakanin likitoci da kwararru kan harkokin kiwon lafiyar jama'a kan wahalar da ke tattare da kididdigar adadin wadanda yakin Isra'ila ya kashe a Gaza, yana mai nuni da cewa ya kamata a yi la'akari da mace-macen kai tsaye da kuma wanda ba kai tsaye ba wato abinda ake kira Indirect.
A halin da ake ciki kuma, kidayar wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata ya zama da wahala ga ma'aikatar lafiya ta Falasdinu yayin da ake ci gaba da gwabzawa.
A al'adance ma'aikatar ta dogara ne da bayanan jami'an asibiti a yankin da aka yi wa kawanya, wadanda ke karbar wadanda suka jikkata da kuma gawarwakin wadanda suka mutu.
Duk da haka, hare haren na Isra'ila sun lalata yawancin asibitocin Gaza, kuma sun durkusar da tsarin kiwon lafiya a asibitocin na Gaza.
Akalla Falasdinawa 100 ne aka kashe a ranar 10 ga watan Agusta a wani kisan gilla da sojojin Isra’ila suka yi a makarantar Al-Tabi’in ta birnin Gaza.
Wakilin gidan Jaridar Al_Mayadeen a Gaza ya ba da rahoton wahalar kidayar mutanen da suka yi shahada sakamakon tarwatsewar da jikkunan mutane suka yi sai dai aka riƙa auna kilo 70 a matsayin Shahidi ɗaya.
0 Comments