Murna Kan Kisan Haniyeh Ta Rikiɗe Zuwa Firgici Sakamakon Zaɓen Yahya Sinwar A Matsayin Sabon Shugaban Hamas.

 


Daga - Muhammad Attahiru. 

Zaɓen Yahya Sinwar a matsayin sabon shugaban ofishin siyasa na Hamas ya girgiza Isra'ila da ƙawayenta na Yamma da yankin gabas ta tsakiya tare da nuna kyakyawar haɗin kai a tsakanin Falasɗinawa.


Hamas ta zaɓi Yahaya Sinwar domin  jagorantar gwagwarmayar siyasar na Hamas. Sinwar shine yanzu ya gaji Ismail Haniyeh wanda Isra'ila ta kashe mako guda da ya gabata.  


Isra'ila ta kashe Haniyeh ne a Tehran dake Iran a ranar 31 ga watan Yuli. 


Haniyeh dai ya tafi Iran ne don halartar bikin rantsar da zaɓeɓɓen shugaban ƙasar, wato Masoud Pezeshkian. 


"Ƙungiyar gwagwarmayar na Hamas ne ta sanar da zaben Kwamanda Yahya Sinwar a matsayin shugaban ofishin siyasa na ƙungiyar, wanda ya gaji shahidi Isma'il haniya. Kamar yadda Hamas ɗin ta fitar a wani sanarwa.

Kakakin na Hamas, Osama Hamdan ya bayyana a ranar Talata da ta gabata cewa, Sinwar zai lura da abin da ya shafi ci gaba da tattaunawa domin ganin an tsagaita buɗe wuta. Sai dai ya ci gaba da cewa, "Matsalar dake tattare da tattaunawar ba daga Hamas ba ne," kamar yadda Hamdan kakakin na Hamas ya shaidawa Al Jazeera. 


Har wala yau ya zargi Isra'ila da ƙawayenta Amurka da gazawa wajen kawo natijar yarjejeniyar na tsagaita wuta. 


Kakakin na Hamas ya bayyana cewa, wannan dalilin yasa kungiyar na Hamas ta tsaya tsayin daka a fagen fama da kuma siyasa. Inda ya kuma kara da cewa, "wanda aka baiwa jagoranci a yau shi ne wanda ya jagoranci yakin sama da kwanaki 305 kuma har yanzu yana nan a fagen fama."


Sabon kwamandan na Hamas wato Yahaya Sinwar ne ya shirya wani harin ba-zata da ƙungiyar Hamas ta kai a kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Harin da ya yi silar kashe mutane 1,100 wanda aka yi wa laƙabi da guguwar Al-Aqsa tare da kama yahudawa kimanin mutum 250. 


Bayan farmakin dai Isra'ila ta kaddamar da yaki a kan Gaza. Inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 39,700 a Gaza, ciki har da yara fiye da 16,000 zuwa yauzu da muke haɗa wannan rahoto.  


Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya sha nanata cewa manufar wannan harin shine Hamas ta saki mutanen da take tsare da su da kuma ƙoƙarin ganin bayan kungiyar na Hamas.  


Aƙalla sama da mutane 100 da aka yi garkuwa da su aka sako tun bayan yarjejeniyar sulhu da Hamas a watan Nuwamban bara. Hakazalika an kashe mutane da dama daga cikin fursunonin yayin munanen hare-haren da Isra'ila ke kaddamarwa a zirin Gaza. 


Sai dai duk da haka, alƙawarin da Isra'ila ta yi na shafe Hamas ya ci tura. Domin gwamnatin Netanyahu ta gaza kame Sinwar a cikin watanni 10 da suka gabata duk da ruguza mafi yawan yankin na Gaza.


FALASDINAWA SUN YI MARABA DA NAƊIN SINWAR


Wani bafalasɗine Hani al-Qano, da ke gudun hijira a Deir el-Balah, ya yaba da zaben Sinwar a matsayin sabon shugaban siyasar Hamas, yana mai cewa hakan zai kawo kalubale ga Isra'ila.


Inda ya bayyana cewa, Sinwar zai yi tasiri sosai wajen shawarwarin da zasu kawo sauyi, hakazalika zai kasance kalubale ga Isra'ila, bisa lura da cewa Sinwar na zaune ne a cikin zirin Gaza tare da mutanen da aka yi wa ƙawanya. 


Falasɗinawa mazauna Yammacin Kogin Jordan sun nuna ƙarin sha'awa ga naɗin Sinwar. Farah Qassem, wani mai shagon sayar da kofi a Ramallah ya shaidawa AFP cewa "Zabar Sinwar ya jagoranci kungiyar Hamas wata kyakkyawar shawara ce domin Sinwar na zaune ne a tsakiyar yaƙin, saboda haka ya san ainihin abin da yake gudana." 


Emad Abu Fokheidah, wani jami'in makaranta a yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, shi ma ya bayyana mahimmancin tsayar da Yahaya Sinwar saboda tsayin dakarsa a tunkarar ayyukan ta'addancin Isra'ila.


Abu Fokheidah ya ce, "Zabar Sinwar shawara ce ta hikima da kuma saƙo ga mamayar Isra'ila cewa, mafita ta  siyasa wadda Isra'ila ta ƙi amincewa da shi ta hanyar kashe Ismail Haniyeh, zai samu ne kawai daga bakin bindiga." 


FIRGICI YA BAZU A ISRA'ILA


Shawarar da Hamas tayi na nada Sinwar a matsayin sabon shugabanta na siyasa, ya yaɗa tsoro mai tsanani a tsakanin Isra'ilawa. 


Kakakin sojin Isra'ila Rear Adm Daniel Hagari ya yi barazanar kashe Sinwar. Tun biyo bayan fara yaƙin na Gaza. Isra'ila ta fake da farmakan kungiyar Hamas inda ta kashe dubban Falasɗinawa da sunan kai wa ƙungiyar na Hamas hari. 


Barazanar Hagari ka iya zama wani sabon uzuri ga Isra’ila na yin sabon kisan kiyashi a yunkurin nuna gazawarta na kashe Sinwar da sauran dakarun na Hamas kamar yadda tayi ta yi a tsawon wannan lokaci.


Jama'a a Isra'ila sun nuna damuwa sosai game da naɗin Sinwar. "Sinwar mutum ne mai kwarewa sosai. Ya kasance a kurkukun Isra’ila, ya san Ibrananci, ya san makiyinsa, wanda a zahiri mu ne,” in ji Sagie Havshosh, wani dalibi dan Isra’ila da ke a Kudus (al-Quds).


HAMAS NA DA FAƊIN GASKE:


Yahaya Sinwar mai shekaru 61 da haihuwa, wanda ya zama shugaban Hamas a zirin Gaza a shekarar 2017, ya shugabanci yankin a cikin shekaru da suka gabata. 


Ko da yake shugaba Mahmoud Abbas ya kasance shugaba maras farin jini a tsakanin Falasdinawa, yayin da Sinwar kuwa ya kasance shugaba mai kwarjini da farin jininsa ya ƙaru tun bayan lokacin da Isra'ila ta kaddamar da yakin kisan ƙare dangi a Gaza. 


Maye gurbin Haniyeh da Sinwar ya bayyana a fili cewa zai taka muhimmiyar rawa a hangen nesa na Hamas, kamar yadda a halin yanzu yake iko da sassan soja da na siyasa na gwagwarmaya. 


Gwamnatin Netanyahu ta kashe Haniyeh ne domin daƙile ƙoƙarin da ake na sasantawa a Gaza. Sai dai daga yanzu Sinwar shine babban mai shiga tsakani da Isra'ila za ta tattauna da shi kan yiwuwar tsagaita buɗe wuta a Gaza da kuma sako sauran mutanen da suka yi garkuwa da su. 


Wannan zai zama mafarki mai maimaitawa ga gwamnatin Netanyahu. A bayyane yake kamar rana cewa yaƙin kisan gillar da Isra'ila take yi a Gaza ya ci tura. 


Gwamnatin Isra'ila ta kashe Haniyeh amma kuma magajinsa ya fi kasancewa mafi tirjiya ga mamayar Isra'ila.


A halin yanzu, Falasɗinawa a Gaza ke da rinjaye yayin da Hamas ta sami damar inganta haɗin kai a tsakanin ɓangarorin siyasa da kuma na sojin ƙungiyar. 


A yanzu zaɓan Sinwar ya aika saƙo mai mahimmanci ga duniya cewa, Hamas za ta ci gaba da zama a Gaza duk da yunkurin Isra'ila na kawar da sabon matsayin na Sinwar. 


Hakan kuma ya kara kunyata gwamnatin Netanyahu ta hanyar bayyana gazawarta na soja da na ƴan leken asiri.


Freedom Fighters Ng🎙️

Post a Comment

0 Comments