Daga - Mahadi Tukur Almizan
Vice Adm. George Wikoff ya bayyana cewa sun kasa gano raunin dakarun Ansarullah na Yemen ballantana sojin na Amurka su riƙa kai masu hari a inda suke da rauni babu ƙaƙƙautawa.
Vice Adm. George ya bayyana cewa dakatar da hare haren Yemenawa ya fi karfin soji kawai, akwai bukatar ayi aiki da wasu hanyoyi fiye da karfin soji, ya bada shawarar Amurka da kawayen ta su nemi wasu hanyoyin da za su takure dakarun na Ansarullah a maimakon amfani da karfin soji kawai.
Aikin da aka baiwa sojin ruwan Amurka na kawo karshen hare haren dakarun Yemen kan jiragen dakon kaya ba za su iya cimma nasara ba su kaɗai cewar kwamanda George Wikoff dake jagorantar sojin Amurka a gabas ta tsakiya ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da kafar yaɗa labarai ta Business Insider news ta wallafa a shafin ta.
Tun lokacin da Isra'ila ta fara kai hare hare kan al'ummar Palasɗinu a Gaza ne dai rundunar sojin Ansarullah na Yemen suka dauki matakin haramta ma jirage shiga tashoshin Isra'ila, kuma suke harar duk wani jirgi da ya saɓa ma wannan matakin na su.
Kuma sun jaddada cewa waɗannan hare haren ba za su tsaya ba har sai Isara'ila ta dakatar da kai hare hare kan al'ummar Palasɗinu a Gaza.
A wajen wani taro da cibiyar 'Center for strategic and international studies' ta shirya a ranar Laraba George Wikoff ya bayyana cewa "Mafita ba zata zo ta hanyar amfani da makamai ba" za a samu mafita ne idan aka samu haɗin kan kasashe domin murkushe dakarun na Ansarullah.
Wikoff ya bayyana cewa "Yawan kasashen da za a samu su shigo cikin lamarin zai samar da wata dama ta diflomasiyya da zata samar da nasara"
"Tabbas mun raina karfin su, kuma babu ja akan wannan, amma mun iya dakatar da su? A'a " cewar George Wikoff
Jami'an Amurka sun bayyana cewa sama da watanni takwas suna aikin baiwa jiragen dakon kaya kariya daga hare haren dakarun na Yemen a tekun Red Sea da mashigar taku ta Aden, amma haryanzu Yemenawa na cigaba da kai hare haren su yadda suke so.
Domin ko a ranar 19 ga watan da ya gabata na July, sun aika jirgi maras matuƙi yake jar cikin babban birnin Isara'ila wato Tel Aviv yakai hari harma ya kashe wani ba Isra'ile kuma ya raunata wasu da dama.
0 Comments