Daga - Mahadi Tukur Almizan
An samu cutar Polio a karon farko cikin shekaru 25 sakamakon gurbata ruwan zirin Gaza da Isra'ila ta yi.
Hukumar lafiya ta duniya 'WHO' ta tabbatar da cewa wani jariri ɗan kimanin watanni 10 ya kamu da cutar shan inna, kuma wannan shine karo na farko a cikin shekaru sama da 25, shugaban hukumar agajin Palasɗinawa ta majalisar dinkin duniya 'UNRWA' Philippe Lazzarini ya bayyana a jiya juma'a 23 August.
BREAKING: UNRWA reports that the World Health Organization has confirmed a 10-month-old infant in Gaza has been paralyzed by polio, the first case in 25 years. According to the agency, delay in the humanitarian ceasefire could increase the risk of further spread among children. pic.twitter.com/HzIXb40yTj
— Quds News Network (@QudsNen) August 23, 2024
"Bai kamata a bari cutar shan inna 'Polio' ta banbance tsakanin Yaran Palasɗinawa da na Isra'ila ba" cewar Lazzarini a wata sanarwa da ya karanta a farkon gangamin da hukumar ta 'UNRWA' ta yi na neman a baiwa Yaran Palasɗinawa a Gaza riga kafin Polio ta hannun asibitocin 'WHO' da ma'aikatan su dake zagayawa.
Ya kara da cewa "Jinkirin samar da tallafin riga kafin zai yaɗa cutar a tsakanin sauran yaran Palasɗinawa"
"Bai wadata kawai a kawo riga kafi zuwa Gaza ba, domin samar da sauyi dole ne riga-kafin ya shiga bakin kowane Yaro daga Yaran Palasɗinawa wanda bai wuce shekara 10 ba" a cewar Lazzarini
Hukumar sojin Isra'ila mai kula da al'amarin fararen hular Palasɗinawa 'COGAT' ta sanar a makon da ya gabata cewa "Muna kokarin tallafawa da riga kafi" a cewar sojin sun fara yin riga kafin a tsakanin sojin na Isra'ila kuma wai suna kokarin ganin riga kafin ya shiga zirin Gaza.
Cutar ta Polio dai cuta ce mai haɗari dake yaɗuwa a cikin gurbataccen abinci ko ruwa, tafi kama yara ƴan tsakanin shekaru biyar, cutar tafi kashe ƙananan Yaran masu karancin shekaru sakamakon matsalar numfashi.
Tuntuni dai ma'aikatar lafiya ta Gaza ta yi gargaɗin yaɗuwar wannan cuta, sakamakon rashin riga kafi da kuma karancin wuraren kulawa da marasa lafiya.
"No matter how much I talk about this crime, it cannot be described."
— Quds News Network (@QudsNen) August 10, 2024
The head of emergency services in northern Gaza reports on the horrific Israeli massacre at Al-Tabi'in School, where Israeli airstrikes slaughtered at least 100 Palestinians, including women and children, as… pic.twitter.com/obcVPerdDq
0 Comments