Yarinya Ƴar Shekara 9 Da Wasu Yara Biyu Sun Isa South Africa Domin Samun Kulawar Likitoci

 


Mira mai kimanin shekaru 9 da ta samu munanan raunuka sakamakon harin jiragen Isra'ila ta samu kyakkyawar tarba yayin da ta iso birnin Johannesburg na ƙasar Afirka ta kudu.

 

Mira ta iso babban birnin ƙasar ta Afirka ta Kudu a yau juma'a domin neman lafiya.



Mira za ta haɗu da wasu yara biyu masu munanan raunuka da suka samu sakamakon harin jiragen Isra'ila a Gaza, ɗaya mai kimanin shekara 1 mai suna Sanad da wata mai suna Lina ƴar kimanin shekaru 17, dukkanin su za su karɓi kulawar likitoci.



Dandazon al'ummar Johannesburg ne suka taro domin gaishe da Mira a filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa OR Tambo International Airport dake birnin, a kusa da Asibitin da za a yi masu gyaran karaya da wasu raunuka masu alaƙa da ƙashi.



Mutane takwas ne suka raka Mira wanda suka haɗa da mahaifanta da ƴan uwanta.


Wannan shine karon farko da aka kawo masu raunuka irin na su zuwa ƙasar ta Afirka ta Kudu daga Gaza, ƙungiyar tallafawa Yaran Palasɗinawa mai suna 'Palestinian Children's Relief Fund (PCRF' ne suka yi kokarin kawo Yaran zuwa Afirka ta Kudu domin samun kulawar likitoci.


Daga January zuwa yau ƙungiyar ta PCRF ta yi sanadiyyar fitar da Yaran Palasɗinawa 120 daga Gaza zuwa Amurka da wasu ƙasashe a Gabas ta tsakiya da wasu ƙasashen Turai.

Post a Comment

0 Comments