Daga - Mahadi Tukur Almizan
Ƴan muqawama na Palasdinawa sun yi artabu da sojin Isra'ila wajen baiwa birnin Jenin , Tulkarem da Nablus Kariya daga hare haren Isra'ila a ranar Laraba.
A arewacin yammacin gabar kogin Jordan ƴan muqawamar sun yi musayar wuta da sojin na Isra'ila na sama da mako guda.
Al-Quds Brigade tsagin masu makamai na ƙungiyar 'Palestinian Islamic Jihad' (PIJ) ne suke jagorantar yaƙar sojin na Isra'ila inda aka samu musayar wuta sau 14 cikin kwanaki 3 a tsakanin sojin na Isra'ila da ƴan muqawama.
Ƴan muqawamar sun dasa abubuwan fashewa a wurare mabanbanta da suka tashi da sojin na Isra'ila a birnin na Jenin.
Sashen labarai na rundunar ta al-Quds Brigade sun bayyana cewa waɗannan abubuwan fashewar da suka dasa sun kashe sojin na Isra'ila da yawa kuma sun raunata wasu.
Hakanan tsagin rundunar na Tulkarem sun bayyana cewa sun yi ma sojin na Isra'ila kwanton ɓauna a unguwar al-Balawna, inda anan ma suka kashe sojin na Isra'ila kuma suka raunata masu yawa.
Hakanan kuma dai a Tulkarem ɗin ƴan muqawamar sun dasa abubuwan fashewa sannan kuma sun yi musayar wuta har sau 7 da sojin na Isra'ila.
Hakanan suma ƴan muqawamar na birnin Nablus 'Nablus Brigade' sun yi musayar wuta da sojin na Isra'ila har sau 4, kuma sun dasa abun fashewa guda 1.
Hakanan wasu rundunonin ƴan muqawama har 7 sun sanar da hare haren da suka ƙaddamar a West Bank, ciki da Fatah al-Intifada inda masu makamai na ƙungiyar ta Intifada da ake kira 'al-Aasifa Forces suka yi artabu da sojin Isra'ila a Tulkarem.
Rundunar al-Aqsa Matyrs Brigade a Nablus sun dasa abubuwan fashewa wanda suka tashi da sojin na Isra'ila a Layi na 16 dake birnin Nablus.
Hakanan Qassam Brigade na ƙungiyar Hamas sun bayyana cewa dakarun ta da na wasu rundunonin muqawama sun yi ma sojin Isra'ila gagarumar asara a sansanin gudun hijira na 'Tulkarem Refugee Camp'.
A ranar 28 ga watan August ne sojin Isra'ila suka ƙaddamar da wani gagarumin hari a West Bank wanda ya kashe gomomin Palasɗinawa tare da raunata wasu masu yawa da lalata kayayyakin more rayuwa.
0 Comments