Hezbollah Ta Hari Hedikwatar Hukumar Leƙen Asirin Isra'ila 'Mossad' Dake Tel Aviv A Jiya Laraba

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Ƙungiyar ƴan muqawama ta kai zafafan hare hare kan Hedikwatar hukumar leƙen asirin Isra'ila da ake kira Mossad domin kariya ga ƙasar Lebanon da kuma goyon bayan al'ummar Palasɗinu.


Sashen yaɗa labarai na ƙungiyar ta Hezbollah ya fitar da jerin sanarwoyi masu ɗauke da bayanan hare haren da ƙungiyar ta kai a jiya Laraba da kuma ɓarnar da suka yi ma maƙiya.


Hari na farko


Hezbollah ta fara da harar sansanin sojin Isra'ila da ake kira 'Ilaniya Base', sun hari wannan sansani da missile da mai suna 'Fadi -1'.


Sai kuma hari na biyu

Da misalin ƙarfe 6:30 na safiyar jiya dakarun Hezbollah suka harba Ballistic Missile mai suna 'Qader -1' zuwa Hedikwatar Mossad dake   Tel Aviv, wannan Hedikwatar ita ce ke da alhakin kashe kwamandojin Hezbollah da kuma harin Pagers da Isra'ila ta yi a Lebanon cikin makon da ya gabata.



Hari na uku

Dakarun na Hezbollah sun kai hari na uku ne kan ƴan share wuri zauna  da ake kira Settlers a Hatzor, sun harba gomomin roka.


Hari na huɗu

Sun kai hari na huɗu ne a sansanin sojin Isra'ila da ake kira 'Dado Base' inda suka harba gomomin missiles

Post a Comment

0 Comments