Isra'ila Ta Kai Hari Kudancin Birnin Beirut Na Lebanon A Jiya Juma'a, Har An Samu Shahidai.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Isra'ila ta yi iƙirarin cewa wai ta kai harin ne kan Ibrahim Aqeel Kwamandan rundunar Hezbollah ta musamman da ake kira 'Jaish Ridwan' da turanci kuma 'Redwan Forces'


Jiragen yaƙin Isra'ila sun hari tsakiyar kudancin birnin Beirut babban birnin ƙasar Lebanon, harin ya tarwatsa muhallai biyu a yau juma'a 20 ga watan Satumba.


Aƙalla mutum 9 ne suka yi shahada zuwa yanzu kuma samu gomomi masu raunuka ciki harda ƙananan yara da mata.


Kafafen yada labaran Isra'ila sun yi ikirarin cewa Isra'ila ta nufi Kwamandan Jaish Ridwan Ibrahim Aqil ne wanda ya gaji matsayin Sahaheed Fu'ad Shukr, wanda Isra'ila ta kashe a wani hari makamancin wannan a watan July.


Wannan hari ya biyo bayan hare haren da Isra'ila ta ƙaddamar wanda ta dasa abubuwan fashewa a kayayyakin sadarwa na soji da fararen hula a ƙasar ta Lebanon wanda yayi sanadiyyar shahadar mutum 37 kuma ya raunata dubunnai.


Wakilin kafar yaɗa labarai ta Almayadeen ya bayyana cewa har da ƙananan yara cikin waɗanda harin ya shafa, wanda Isra'ila ta jefa missiles guda 4 a gine ginen dake unguwar al-Qa'im dake kudancin birnin Beirut.



Bayan harin wani jami'in haramtacciyar ƙasar Isra'ila ya zanta da gidan Talabijin na Kann Tv ya bayyana cewa "Babu sauran wani jan layi a wannan yaƙin" kuma ya sanar cewa Netanyahu ya soke tafiyar da zai yi zuwa Amurka saboda rincaɓewar yanayi tsakanin Isra'ila da Hezbollah.


Jim kaɗan bayan kai harin mai magana da yawun ministan tsaron Amurka John Kirby ya bayyana cewa Isra'ila bata sanar da Amurka cewa zata kai wannan hari ba kafin ta kai.


Wani Farfesa daga jami'ar Amurka dake Beirut 'American University Of Beirut ' mai suna Rami Khoury ya bayyana cewa Isra'ila na son faɗaɗa yaƙi da Hezbollah da nufin cewa zata yi nasara akan Hezbollah ɗin, sai dai sun gwada hakan lokuta mabanbanta basu yi nasara ba.

Post a Comment

0 Comments