Daga - Mahadi Tukur Almizan
An raba su da muhallan su, sun koma rayuwa a cikin makarantu, kuma an bi su cikin makarantar da suka samu mafaka an kashe su an raunata su.
A jiya Alhamis 26 ga watan Satumba da muke ciki haramtacciyar ƙasar Isra'ila ta kai wani mummunan hari makarantar Hafsa al-Fulaja dake sansanin gudun hijira na 'Jabalia Refugee Camp' a arewacin Gaza
Wannan makaranta dai ta zama muhallin da iyalan Palasɗinawa da aka raba da muhallan su ke rayuwa.
Saboda tsabagen ta'addanci da rashin hankali sojin Isra'ila sun bayyana cewa sun kai hari makarantar ne wasu saboda sun gano cewa Hamas na aiki da makarantar a matsayin 'Command and control center'
Ba wannan bane karon farko da Isra'ila ke kai hare hare asibitoci da makarantu ba, wanda suka zame ma Palasɗinawan wurin zama sakamakon rasa muhallan su da suka yi saboda hare haren ta'addancin Isra'ila, kuma a kodayaushe suka kai hare haka suke cewa wai Hamas na aiki da muhallan
مجزرة يرتكبها الاحتلال الإسرائيلي بحق النازحين في مدرسة الفالوجا بمخيم جباليا شمال قطاع غزة pic.twitter.com/bOmPuE9kJx
— أنس الشريف Anas Al-Sharif (@AnasAlSharif0) September 26, 2024
Ko a ranar 21 ga wannan wata na Satumba wato kwanaki 6 da suka gabata, haramtacciyar ƙasar ta Isra'ila ta kai irin wannan hari a wata makaranta da Palasɗinawan ke zaune, wanda ya kashe mutane 22, cikin su har da ƙananan Yara 13, mata 6, kai harma da jariri ɗan wata uku a cewar ofishin yaɗa labarai na Gwamna Gaza.
Kaso 90 na mutanen Gaza wanda adadin su yakai mutum miliyan 2.3 ne hare haren ta'addancin Isra'ila suka raba da muhallan su cikin ƙasa da shekara 1 a Gaza, hare haren da suka yi sanadiyyar rasa rayukan Palasɗinawa 41,000 wanda mafi yawan su mata ne da ƙananan Yara.
Wannan harin ta'addancin da Isra'ila ta kai sansanin gudun hijirar na Jabalia ya biyo bayan kwana ɗaya da Isra'ila ta kawo gawarwakin Palasɗinawa 88 da ta kashe waɗanda ba a iya gane ko su waye ba sakamakon har sun fara ruɓewa a shekaranjiya Laraba.
Scenes from a holocaust. The German-backed Zionist genocide regime dumped 88 Palestinian bodies in Gaza that it had been withholding for months, with no identification of who they are. The health ministry in Gaza is refusing to bury them without the enemy providing information… https://t.co/3cFY7NmUhV
— Ali Abunimah (@AliAbunimah) September 26, 2024
0 Comments