Daga - Mahadi Tukur Almizan
Binciken da rundunar ta fitar ya nuna cewa ba maƙiya bane suka harbo jirgin, wai haɗari ne jirgin yayi
Sojin Isra'ila 2 ne suka yi mutu wasu kuma dayawa sun samu raunuka sakamakon fadowar jirgin sojin a kudancin a safiyar ranar Laraba 11 ga watan Satumba da muke ciki.
Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta bayyana cewa jirgin rundunar sojin saman haramtacciyar ƙasar ta Isra'ila yayi haɗari ƙirar 'Black Hawk Helicopter', zuwa yanzu binciken su ya nuna cewa ba harbo jirgin aka yi ba, amma ana cigaba da binciken abinda ya haddasa haɗarin.
Rundunar ta bayyana cewa an sanar da iyalan waɗanda suka mutu, wanda dukkanin su suna aiki ne Unit 669 na rundunar sojin saman Isra'ila.
Sojin Isra'ila bakwai ne suka samu raunuka sakamakon fadowar jirgin.
Jirgin dai yana shawagi ne a sararin samaniyar kudancin Gaza yana dauke da jami'an lafiya na rundunar sojin, yayinda suke kokarin kai ma wani sojin Isra'ila da ya samu mummunan rauni a wata musayar wuta da suka yi da ƴan muqawama na Palasɗinawa.
Jirgin ya faɗo ne a yayin da yake kokarin sauka a sansanin sojin na Isra'ila dake Rafah, sai dai jirgin ya yi mummunar faduwa domin kuwa ya yi kaca kaca.
Faduwar jirgin ta zo dadai lokacin da sojin na Isra'ila ke cigaba da ta'addanci kan al'ummar Palasɗinu a zirin Gaza.
A ranar 11 ga watan na Satumba da muke ciki jirgin ya faɗo kafar yaɗa labarai ta Palasɗinawa WAFA News Agency ta wallafa labarin cewa jirgin yaƙin sojin Isra'ila ya kai hari gidan iyalin Abu Shalouf dake Al-Mawasi kusa da Rafah, wanda yayi sanadiyyar shahadar Palasɗinawa 4 kuma ya raunata wasu mutum 15.
Hakanan kwana ɗaya kafin wannan ranar sojin na Isra'ila sun aikata wani kisan kiyashi a Gaza wanda hukumar Civil Defense ta Gaza ta bayyana a matsayin ɗaya daga cikin kisan kiyashi mafi muni tun daga karshen watan Agusta.
Aƙalla Palasɗinawa 40 suka yi shahada sannan wasu kimanin mutum 60 suka samu raunuka a wannan kisan kiyashi da suka yi a sansanin gudun hijira na Al-Mawasi.
Hukumar ta Civil Defense ta bayyana cewa wannan harin ya share iyalai da dama daga doron ƙasa.
0 Comments