Daga - Mahadi Tukur Almizan
A jiya Talata ne aka cika kwanaki 354 da fara ta'addancin Isra'ila a Gaza, har yanzu Isra'ila na cigaba da ta'asa.
A birnin Khan Yunis dake kudancin zirin Gaza jami'an hukumar Civil Defense na Palasɗinawa sun yi nasarar zaƙulo gawarwakin aƙalla shahidai 7 da suka yi shahada sakamakon harin da Isra'ila ta kaima wasu gidaje biyu.
Injuries among Palestinian civilians were transported to a hospital following an Israeli bombardment targeting a home belonging to the Abu Harb family in Qeezan Al-Najar in Khan Younis. pic.twitter.com/ZhLSvyAsxZ
— Quds News Network (@QudsNen) September 24, 2024
Hakanan jami'an na hukumar ta Civil Defense sun zaƙulo gawarwakin wasu Shahidai 5 da masu raunuka sama da 10 a unguwar Qizan al-Najjar, hakanan sun zaƙulo wasu Shahidai 2 da masu raunuka 5 a wani gida dake unguwar Tahlia Area.
Hakanan an tabbatar da samun shahidai aƙalla 2 da masu raunuka sakamakon Boma boman da Isra'ila ta jefa a wani gida dake unguwar Sheikh Nasser a birnin na Khan Yunis.
Hakanan jirgin Isra'ila yayi harbe harbe a sararin samaniyar unguwar Mawasi dake yammacin birnin Khan Yuni.
Haka kuma a tsakiyar zirin Gaza motocin sojin na Isra'ila sun buɗe wuta a arewa maso gabashin sansanin gudun hijira na Al-Bureij.
Hakanan a arewa maso gabashin birnin na Gaza sojin haramtacciyar ƙasar ta Isra'ila sun tarwatsa gine gine a kudancin unguwar Al-Sabra, hakanan sun hari dandalin Abu Sharia Square.
A arewacin zirin na Gaza ma sojin na Isra'ila sun ƙaddamar da hare hare a birnin Bin Lahia.
An kara adadin waɗannan shahidai da masu raunuka kan adadin Shahidai 41,455 da masu raunuka 9587 adadin da aka iya taskace wa tun daga ranar 07 ga watan Oktoban shekarar 2023 kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Palasɗinawa ta fitar da alƙaluman.
Wannan yana nufin har yanzu akwai wani adadi mai yawa na mutanen da ɓaraguzan gine gine suka danne da kuma waɗanda da jami'an agaji da motocin su suka kasa isa gare su domin kai masu ɗauki
0 Comments