Masu Zanga Zanga A Canada Da Amurka Sunyi Kiran A Dakatar Da Kashe Palasɗinawa Da Al'ummar Lebanon



Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Dubunnan masu zanga zanga ne suka cika titunan birnin New York na ƙasar Amurka suna ɗaga murya suna Allah wadai da kisan kiyashin da Isra'ila ke cigaba da yi kan al'ummar Palasɗinu, da kuma hare haren ta'addanci kan al'ummar Lebanon.


Mafi yawan masu zanga zangar sun daɗe suna fitowa tsawon watanni suna bayyana damuwar su akan wannan aika aika suna kiran a dakatar da Isra'ila daga cigaba da aikata wannan ta'addanci.


Jami'an ƴan sandan birnin New York (NYPD) sun fito sanye da hular kwano suna cikin shirin jiran kota kwana, suna ankare da masu zanga zangar wato dai sun shirya arangama da masu zanga zangar sun shirya sa ƙarfi domin murkushe zanga zangar idan hakan ta kama.


A can birnin Washington DC ma dubunnan masu zanga zangar ne suka fito suna kiran Amurka ta dakatar da tallafin da take baiwa Isra'ila na makamai da ƙarfin soji, wanda suka kira hakan laifin yaƙi.


Yawan masu zanga zangar da irin kalaman da suke furtawa ya nuna fushin su da ƙarin yawaitar masu kiran Amurka ta canza salon siyasar ta da Gabas ta tsakiya.

Masu zanga zangar da suka ɗakko tun daga fadar mulkin Amurka da ake kira 'White House' har birnin Washington a daren ranar talata sun riƙa faɗin "Hands Off Lebanon" suna nuna damuwar su da goyon bayan su ga al'ummar gabashin Asia suna faɗin cewa "Daga Gaza zuwa Beirut, Gaisuwar Girmamawa Ga Shahidan Mu".

👉

Sun nemi shugaban Amurka Joe Biden ya gaggauta dakatar da tallafin makaman da Amurka za ta tura ma Isra'ila.

Post a Comment

0 Comments