Sabon Kisan Kiyashin Isra'ila A Sansanin Gudun Hijira Na Al-Bureij



Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Jiragen yaƙin Isra'ila sun aikata kisan kiyashi kan fararen hula.


Gomomin Palasɗinawa ne suka maƙale a ɓaraguzan gine ginen da boma boman jiragen yaƙin Isra'ila suka rusa a sansanin gudun hijira na 'Al-Bureij Refugee Camp'


Sojin na Isra'ila sun aikata kisan kiyashin ne a ranar 17 ga watan Satumba da muke ciki wanda yabar gomomin Palasɗinawa da raunuka a sansanin dake tsakiyar zirin Gaza.



Sansanin da Isra'ila ta hara yana cike da ɗimbin mutane

Hukumar Civil Defense ta Palasɗinawa ta bayyana cewa akwai Palasɗinawa sama da 50 a cikin gidajen da Isra'ila ta jefa ma Bom.


"Ƴan mamayar sun yi amfani da makaman da Amurka ke basu wajen kai wannan hari kan fararen hula" hukumar ta nemi agajin babbar hukumar agaji ta duniya 'International Red Cross' domin zaƙulo mutanen da suka maƙale a ɓaraguzan gine gine.


Ma'aikatar lafiya ta Palasɗinawa ta bayyana cewa aƙalla Palasɗinawa 23 harin ya kashe ya raunata wasu 50 a sansanin na Al-Bureij.


"Ƴan mamayar sun jefa boma bomai a gidaje mabanbanta wanda suka haɗa da gidan iyalan Al-Tarturi, Abu Shawqa da Al-Batran duka a sansanin na Al-Bureij, kuma haryanzu akwai gomomi a ƙarƙashin ƙasa da ɓaraguzan gini ya danne " kamar yadda ma'aikatan lafiya suka bayyana ma kafar yaɗa labarai ta WAFA News Agency.



Ƙungiyoyin ƴan muqawama na Palasɗinawa sun yi Allah wadai da wannan kisan kiyashi.


Kungiyar 'Mujahideen Movement' ta bayyana cewa "Shirun al'ummar duniya da gazawar larabawa wajen taimaka ma Palasɗinawa shi ne yake baiwa Isra'ila ƙwarin gwuiwar cigaba da aikata wannan ta'addanci kan al'ummar Palasɗinu".


Itama ƙungiyar Hamas ta yi Allah wadai da wannan kisan kiyashi inda ta bayyana cewa wannan ta'addanci yazo ne a daidai lokacin da duniya tayi shiru, sannan masu riƙe da dokokin ƙasashen duniya sun kasa yin abinda ya hau kan su na yin amfani da dokokin kare fararen hula a lokacin yaƙi.

Post a Comment

0 Comments