Sama Da Ɗalibai 11,000 Isra'ila Ta Kashe A Gaza Cikin Ƙasa Da Shekara Ɗaya.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan 

A maimakon mayar da hankali wajen neman ilimi yanzu ƙananan yara na gwagwarmayar neman tsira ne a Gaza.


A ranar Laraba 17 ga watan Satumba da muke ciki ma'aikatar ilimi ta Palasɗinawa ta bayyana cewa ɗalibai 11,001 hare haren ta'addancin Isra'ila suka shahadantar wasu ɗalibai 17,772 sun samu raunuka a zirin Gaza da yammacin gaɓar kogin Jordan (West Bank) tun daga fara wannan ta'addanci a watan Oktoba na bara.


A yammacin gaɓar kogin Jordan sojin na Isra'ila sun kashe ɗalibai 113, sun raunata 548, sun kama 429.


Ana dab da cika watanni 12 da fara wannan ta'addanci kan al'ummar Palasɗinu, wanda ya raba ɗalibai 625,000 da makarantun su, yanzu kuma ana fuskantar barazanar shiga shekara ta biyu a cikin wannan yanayi.


Da ace komai na tafiya daidai to da a cikin wannan wata na Satumba aƙalla yara 45,000 ne za su fara shekarar su ta farko a makaranta, sai yanzu babu wannan damar.


Wasu bayanai na hukumar UNICEF sun bayyana cewa rashin damar karatu ga ƙananan yara ta jefa rayuwar yaran cikin wannan mummunan yanayi, iyayen yara sun bada rahoton yadda hakan ya shafi walwalar yara har takaiga abun ya shafi lafiyar su musamman ƙwaƙwalen su sakamakon kaɗaici da rashin walwala.


UNICEF ta bayyana cewa "Yara a zirin Gaza sun rasa gidajen su, dangin su da abokanan su, walwalar su da jin daɗin su, wannan yanayin ya jefa goben su cikin haɗari"  duk a dalilin ta'addancin Isra'ila.


A yanzu dai makarantu a Gaza sun zama muhallan rayuwar al'ummar da aka raba da gidajen su.


Duk da cewa Isra'ila bata ƙyale su ba, domin kuwa Isra'ila ta aikata kisan kiyashi mabanbanta a makarantun da Palasɗinawa ke zaune domin neman mafaka.


Ko a makon da ya gabata Isra'ila ta kai hari wata makarantar majalisar ɗinkin duniya da Palasɗinawa suka mayar sansanin gudun hijira da ake kira Nuseirat Camp a tsakiyar Gaza.


Wannan yasa a maimakon gwagwarmayar neman ilimi yanzu gwagwarmayar neman tsira kawai ɗalibai Palasɗinawa suke.


Kafar yaɗa labarai ta CNN ta wallafa wani rahoto inda ta bayyana cewa ɗalibai suna ɓata mafiyawan lokutan su wajen bin layin neman ruwa da abinci, wanda suka yi matuƙar karanci a zirin na Gaza sakamakon toshe hanyoyin shigar tallafi da Isra'ila ta yi..


"Nayi burin kammala karatuna in taimaki mahaifina wajen ciyar da ahalin mu" cewar wata ɗalibar English Literature mai su Raghad Ezzat Hamouda wadda ke gudun hijira a arewacin Gaza.


Ta kara da cewa "Wannan yaƙin ya rusa man dukkanin buri na, yanzu babu abinda ya rage" ta yi wannan zantuka ne ga kafar taɗa labarai ta CNN


Hakanan ita ma Maryam Shtawi ta bayyana ma CNN cewa "Mun kasance muna karatu, muna halartar azuzuwa, muna yin aikin gida (Homework), muna rayuwar mu cikin farin ciki, amma wannan yaƙin ya rabamu da muhallan mu, yanzu babu sauran neman ilimi, rayuwar mu ta koma yawon ɗiban ruwa da neman abinci, amma ni dai inason karatu".

Post a Comment

0 Comments