Sojin Isra'ila Sun Harbe Ƴata Lokacin Da Ta Leƙo Ta Taga Yayinda Suka Zagaye Unguwar Mu - Mahaifin yarinya ƴar shekara 16 da sojin Isra'ila suka harbe.

 



Daga - Abdurrahman Bala Idris/ Mahadi Tukur Almizan

 Yarinyar 'yar shekara 16 a birnin Jenin ta hadu da ajalinta ne lokacin da wani Sniper na HKI ya harbeta bayan ta leko ta taga.

Lamarin da ke nuni da yadda wasu maharba 'yan Isra'ila ke kaiwa fararen hula hari a yammacin gabar kogin Jordan

Mahaifin Lujain Osama Musleh ya bayyana cewa dakarun sojin Isra'ila sun kewaye unguwar su ne  lokacin da suka harbe diyarsa a goshi. 

Osama Musleh ya ce "Ba ta je tsokanar su ba, ba ta yi jifa ba, kuma ba ta dauke da makami," in ji Osama Musleh.

Ya kara da cewa "tana da shekara 16 kacal, abin da kawai ta yi shi ne kallo daga tagar gidansu sai sojan ya ganta ya harbe ta.

Harsashi guda daya  ya doki goshinta.”

 An harbe Lujain a ranar Talata a garin Kafr Dan da ke Jenin, kuma an hana jami'an lafiya su agaza mata sama da rabin awa, haka aka barta har jinin ta ya gama tsiyayewa a cewar ƙungiyar agaji ta Palasɗinawa mai suna 'Palestine Red Crescent'


Hakazalika maharban ɗauki ɗaiɗai (Sniper) na Isra’ila sun kashe Mohammad Kanaan a sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkarem, yayin da aka bugi mahaifinsa a kugu a lokacin da suke tafiya zuwa masallaci tare.

Mazauna yankin sun ba da rahoton cewa, an jibge maharban ɗauki daiɗai (Snipers) na  Isra'ila a ko'ina cikin yankin, inda suke kai wa fararen hula Falasdinawa hari ba tare da nuna banbancewa ba tsakanin ƙananan yara da iyaye.

Ma'aikatan kiwon lafiya a wani asibiti kusa da birnin Jenin da aka yiwa kawanya sun shaida wa AlJazeera cewa suna rufe tagogin dakin bada agajin gaggawa don kare ginin daga harbe harben Snipers ɗin.

Post a Comment

0 Comments