Daga - Mahadi Tukur Almizan
Mazauna West Bank na cigaba da fargabar dawowar sojin Isra'ila a yankin na West Bank da suka mamaye.
Sojin na Isra'ila sun janye daga biranen dake yammacin gabar kogin Jordan wato West Bank wanda suka haɗa da Jenin da Tulkarem a safiyar juma'a 6 ga watan September bayan sun shafe kwanaki goma suna kisan rashin imani wanda ya yi sanadiyyar shahadantar da adadi mai tare da raunata wani adadin mai yawa da kuma lalata kayan more rayuwa.
Shaidar gani da ido ya shaidawa kafar yaɗa labarai ta Anadolu Agency (AA) cewa sojin na Isra'ila sun fice daga sansanin gudun hijira na Tulkarem ƴan awanni bayan sun fice daga birnin Jenin.
Sojin na Isra'ila dai sun yi gagarumar ɓarna a Tulkarem ɗin kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana.
“Press coverage: The effects of the destruction left by the occupation during its aggression on Tulkarm camp.” https://t.co/3EEzl3ZeO4
— 💧Jac 🗝🇵🇸 (@Jaccal68) September 6, 2024
Hakanan kafar yaɗa labarai ta WAFA News Agency ta bayyana cewa " Sojin Isra'ila sun fice daga birnin Jenin da sansanin gudun hijira dake a Jenin ɗin bayan sunyi ɓarna ta tsawon kwanaki goma"
Sai dai mazauna Jenin ɗin sun bayyana tsoron su na tunanin dawowar sojin na Isra'ila birnin saboda "Haryanzu shingen bincike (Checkpoint) ɗin sojin na Isra'ila yana nan, wannan shine dalilin da yasa ake tunanin za su sake dawowa". Kamar yadda WAFA ta wallafa.
Wakilin kafar yaɗa labarai ta Aljazeera ya bayyana cewa "Ƴan mamayar sun janye maharban dauki daidai (Snipers) da suka jibge da sojin kasa da ke cikin sansanin da sauran unguwannin birnin, amma fa sun jibge motocin sojin a shingayen binciken su da suka zagaye birnin".
Wasu bidiyoyi da hotuna da suka karaɗe shafukan sada zumunta sun nuna irin ɓarnar da sojin na Isra'ila suka aikata a birnin na Jenin ciki har da hanyoyi da shaguna, gidajen kallo da shatale-tale (Cinema and Round about) duk an lalata su.
👈فيديو| آثار الدمار الذي أحدثه الاحتلال داخل أحد الشوارع في مخيم جنين شمالي الضفة الغربية المحتلة pic.twitter.com/1Mp1zKHaqn
— المركز الفلسطيني للإعلام (@PalinfoAr) September 6, 2024
Hakanan an ɓata ruwan amfani da hanyoyin ruwa, har Poles na wutar lantarki duk an tono su kamar yadda shaidar gani da ido na kafar yaɗa labarai ta Anadolu Agency ya bayyana
انسحبت قوات الاحتلال من جنين بعد عدوان استمر عشرة أيام، مخلفة وراءها 22 شهيداً، وعشرات الجرحى ودمار هائل في المنطقة. pic.twitter.com/IppP343CJb
— الشؤون العالمية (@mjrdzayr337191) September 6, 2024
A ranar Alhamis ne dai sojin na Isra'ila suka sake shiga Tulkarem bayan sun fice da asubahin ranar, inda suka yi ma wani asibiti ƙawanya a sansanin gudun hijira dake birnin.
A ranar 29 ga watan August ne sojin suka fara janyewa daga sansanin biyo bayan kashe Abu Shujaa kwamandan rundunar ƴan muqawama ta Palasɗinawa 'Quds Brigades'.
0 Comments