Zuwa Yanzu Sama Da Mutum 500 Sun Yi Shahada, Dubunnai Sun Samu Raunuka A Lebanon.



Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Alƙaluman da aka fitar a jiya Talata sun nuna cewa adadin shahidan da aka samu yakai 558.


Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta bayyana cewa akwai ƙananan yara 50 a cikin Shahidan, wanda suka yi shahada sakamakon kisan kiyashin da Isra'ila ta ƙaddamar a ranar Litinin.


Harin na ranar Litinin  ya shiga sahun ɗaya daga cikin ranaku da al'ummar Lebanon suka fuskanci ta'addanci cikin  shekaru talatin da suka gabata.


Wannan harin yazo ne a daidai lokacin da al'ummar Lebanon suka tashi daga ƙauyukan dake kudanci domin samun mafaka daga hare haren Isra'ila, wasu sun samu mafaka a makarantun dake birnin Beirut da kuma birnin Sidon, wadanda basu samu mafaka ba kuma suna kwana a tashoshin motoci, wasu rahotanni kuma sun nuna cewa wasu ɗaruruwa sun haura zuwa Syria.


Waɗannan munanan hare haren na ranar Litinin sun tilasta mazauna kudanci barin muhallan su, wannan yasa har hotels din dake Beirut sun cika da jama'a masu neman mafaka.


Al'ummar birnin Beirut sun baiwa masu neman mafakar muhallai bakin gwargwadon iyawar su, hakanan an kafa wurin dafa abinci a wani tsohon wurin siyar da Iskar Gas domin raba abinci ga masu neman mafakar.


A gabashin birnin Ba'alabak kuwa an labarto cewa an samu cunkoso a gidajen Biredi da wuraren siyen makamashin girki na Gas, a kokarin da mutane suke na tanadin abubuwan buƙata na yau da kullum bisa tsammanin hare haren Isra'ila.


Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa dubunnan mutanen Lebanon ne suka bar muhallan su tun daga ranar Litinin.

Post a Comment

0 Comments