Ƴan Muqawama Na Gaza Sun Sheƙe Sojoji 4 Daga Unit Ɗin Ƙwararrun Maharba Na Sojin Isra'ila

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Sojojin Isra'ila 4 ne suka bakunci lahira yayinda wani soja daya ya tsira da munanan raunuka a karon battar da suka yi tsakanin su da ƴan muqawama jiya Talata a arewacin Gaza, kamar yadda rundunar sojin Isra'ila ta sanar.


A cikin matattun sojojin akwai Captain ɗaya, da Sergeant uku, dukkanin su sun fito ne daga rukunin ƙwararrun maharban ɗaiɗai na sojin Isra'ila wanda ake kira "Ghost Unit" (Refaim).


Haryanzu dai rundunar sojin Isra'ila na binciken yadda ƴan muqawamar suka halaka su.


Dakarun Hamas dake jagorantar rundunonin ƴan muqawamar na Palasɗinawa na cigaba da artabu da sojin na Isra'ila waɗanda suke kokarin ganin bayan sauran Palasɗinawa 300,000 da suka rage a Gaza, wadanda ke rayuwa tsakanin rusassu da ƙonannun gine gine, wannan duk a cikin yunkurin Isra'ila na kaddamar da abinda suka kira "General Plan"


A ranar 19 ga watan da muke cikin na Oktoba ne wata kotun Belgium ta buɗe binciken ta'addanci da laifukan yaƙi da sojin rukunin ƙwararrun maharban "Ghost Unit" ya aikata wanda yake da rijistar ƙasa biyu Isra'ila da Belgium, wanda ya taso a garin Brussels.


Babban mai lauyan gwamnatin ƙasar ta Belgium ne ya buɗe bincike akan sojin bisa zargin buɗe ma fararen hula wuta a Gaza.


Buɗe binciken dai ya biyo bayan zargin da ɗan jarida Younis Tirawi yayi cewa dakarun rukunin na Ghost suna harar fararen hula da gangan.


Tirawi ya bayyana cewa wani jami'i da yake aiki a rukunin ya fitar da dalilai dake tabbatar da yadda jami'an rukunin suka riƙa harbe fararen hula duk da rashin kasancewar su haɗari ga sojojin Isra'ila.


👉


Rukunin ƙwararrun maharban da ake kira "Ghost Unit" ya ƙunshi ƙwararrun maharba 21 wadanda suka fito daga ƙasashe mabanbanta ciki har da Amurka, Faransa, Germany da Belgium.


Tun fara wannan yaƙi maharban ɗaiɗai wato snipers ɗin Isra'ila suke kashe fararen hula musamman ƙananan Yara.


A cikin watan July wani likita mai suna Perlmutter ɗan ƙasar Amurka da yaje aikin agaji a Gaza ya bayyana irin yadda yaga sojojin Isra'ila na kashe kananan yara ta hanyar harbin su a kai da ƙirji.


Yayinda aka tambaye shi cewa ana cewa yara ne mafi yawancin waɗanda sojin ke kashewa ya bada amsa da cewa "Ai kusan duk yara ne, domin kuwa naga kasaasun Yara cikin yanayin da ban taɓa gani ba a gaba ɗaya rayuwa ta, kamar yadda na gani a cikin mako guda a Gaza".


👉


Da aka sake tambayar shi akan me yake nufi da kalmar 'Shredded' da ya rika siffanta yadda yaga yaran, ya bada amsa da cewa "Yana nufin cewa ya gansu jikkunan su sunyi filla filla babu wasu sassa na jikin su, sakamakon yadda hare haren Bom ɗin Isra'ila ya riƙa tarwatsa jikkunan su".


Perlmutter ya ƙara da cewa mafi yawancin yaran da aka kashe an kashe su ne da gangan ta hanyar harbin waɗannan Snipers ɗin.


Ya bayyana cewa "Akwai yaran da snipers ɗin suka harba sau biyu ma"


Yayin da yake wannan maganar wakilin kafar yaɗa labarai ta CBS ya girgiza har yake cewa "Saurara, kana nufin cewa Snipers sun riƙa harbin yara a Gaza?


Sai ya bada amsa da cewa "Tabbas kuwa, domin akwai yaran da har hoton su na ɗauka, an harbe shi da kyau a ƙirji, hakan yasa ma bazan iya ɗora abun awon bugun zuciya (Stethoscope) ɗina a ƙirjin ba, hakanan kuma an harbi yaron a gefen kai, wannan fa duk yaro ɗaya! Babu yadda za a harbi yaro har sau biyu a bisa kuskure daga maharban ɗaiɗai mafiya ƙwarewa a duniya, kuma duka a makasa".

Post a Comment

0 Comments