Anyi Ma Netanyahu Ihu A Taron Tunawa Da Sahayuniyawan Da Suka Mutu A Harin 07 October

 

Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Sojin Isra'ila dai sun kashe dayawa daga cikin mutanen haramtacciyar ƙasar a a ranar 07 ga watan Oktoba na shekarar 2023, a gefe guda kuma Netanyahu na wasa da duk wani yunkuri na dawo da kamammun mutanen su dake hannu Hamas.



Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ya sha kunya a wajen taron tunawa da waɗanda suka mutu sakamakon harin ɗufanul Aqsa a ranar 07 ga watan Oktoba na shekarar 2023, mahalarta taron wadanda sune iyalan matattun ne suka yi ma shi ihu .


Anyi mashi ihun ne a yayin da yake magana a wajen taron da aka gudanar a maƙabartar Mount Herzl a cikin birnin Jerusalem.


Iyalan matattun sun riƙa ihu suna faɗin kaji kunya, a jikin rigunan wasu daga cikin masu ihun an rubuta "We are not together, I'm an Orphan".


A ranar 07 ga watan Oktoba na shekarar da ta gabata ne rundunar Al-Qassam Brigade ta ƙungiyar Hamas da wasu ƙungiyoyin muqawama na Palasɗinawa suka afka sansanonin sojin Isra'ila da wuraren ƴan share wuri zauna inda suka ƙwamushe mutum 240.


A ƙalla Sahayuniyawa 1,200 ne aka kashe a harin, wasu mayaƙan Hamas ne suka kashe su, wasu kuma sojin Isra'ila ne da kan su suka kashe su a abinda ake kira "Friendly Fire" ta hanyar amfani da Drones da Helicopters kuma suka ɗora ma Hamas alhakin mutuwar su.


Netanyahu yayi ta ɓata yunkurin tsagaita wuta da aka yi tayi a lokuta mabanbanta, wanda zai bada damar yin musayar fursunoni tsakanin mutanen na Isra'ila da kuma Palasɗinawa da Isra'ila ke tsare dasu.


Iyalan kamammun sun fusata bisa aniyar Netanyahu ta cigaba da yaƙin.



Sai dai dayawa daga cikin kamammun Isra'ila dake hannun Hamas, Isra'ilar ta kashe kayanta sakamakon Boma boman da suke jefa wa a Gaza da harbe harbe da bindiga wadanda suka kashe Palasɗinawa sama da 41,000.

Post a Comment

0 Comments