Daga - Abdurraham Bala Idris
Dakarun kasar Yemen sun sanar a ranar Talata cewa sun kai farmaki kan wasu jiragen ruwa guda uku da suka karya dokar hana zirga-zirgar jiragen ruwa zuwa tashoshin jiragen ruwa na haramtacciyar kasa.
Kakakin rundunar Sojin, Birgediya Janar Yahya Saree ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka watsa a gidajen talabijin a ranar Litinin.
"An kai wa jirgin ruwan SC Montreal hari a kudancin 'Arabian Sea ' ta hanyar amfani da jirage marasa matuka guda biyu," in ji shi, ya kara da cewa wani jirgin ruwa mai suna "Maersk Kowloon," an kai ma hari ne a cikin tekun na 'Arabian Sea' da makami mai linzami.
👉
⚡️BIG BREAKING
— Iran_Israel War Observor (@News_Observer1) October 29, 2024
Yemeni armed forces:
We targeted the ship “SC MONTREAL” in the southern Arabian Sea with two drones, achieving a precise strike
We targeted the ship “MAERSK KOWLOON” in the Arabian Sea with a cruise missile, achieving a direct hit
We targeted the ship… pic.twitter.com/fFK909qPbc
Ya kuma kara jaddada cewa
"An kai wa jirgin Motaro hari a tekun Bahar Maliya (Red Sea) da Bab al-Mandab da makamai masu linzami mabanbanta."
A halin da ake ciki, Hukumar kula da Harkokin Kasuwancin Ruwa ta Burtaniya (UKMTO) ta bayar da rahoton cewa, an kai hari kan wani jirgin ruwa mai nisan mil 25 kudu da tashar ruwan Bahar Maliya ta Al-Mukha a kudu maso yammacin kasar Yemen.
Dakarun na kai daruruwa hare-hare kan jiragen ruwa da ke tafiya zuwa, ko suka kusanci tashoshin ruwan haramtacciyar ƙasa a yankunan Palasɗinawa da ta mamaye, bayan wasu hare-hare da suke kaiwa haramtacciyar ƙasa kaitsaye tun watan Oktoban bara.
Sun fara kai hare haren ne tun bayan da Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta fara kisan kiyashi a zirin Gaza, tare da tsaurara matakan dakile ta a gabar tekun, da kuma kara kai hare-haren da take kaiwa Lebanon.
"Rundunar sojin na Yemen ta lashi takobin ci gaba hana jiragen ruwan abokan gaba, kuma zasu cigaba da kai hare-hare kan duk wani abu da ke da alaka da 'Isra'ila' a yankunan Palasɗinawa da Isra'ilar tamamaye.
Saree ya kara da cewa Sojojin mu "ba za su tsaya ba har sai an kawo karshen ta'addanci Isra'ila a Gaza da kasar Lebanon.
Kalaman na zuwa ne kwana guda bayan da sojojin suka yi atisayen yaki da mabanbanta, wanda aka yi wa lakabi da "Don Shirya Fuskantar ku."
Saree'i yace hadin gwiwa da sojojin ruwa da na kasa na kasar Yemen din, an gudanar da atisayen ne a matsayin wata hanya ta karfafa mayar da martani ga "Isra'ila" bisa ta'addancin da take ci gaba da yi.
0 Comments