Daga - Mahadi Tukur Almizan
Da sanyin safiyar yau Litinin jirgin yaƙin Isra'ila ya jefa Bom a asibitin dake arewacin Gaza, wanda ya jawo tantunan masu zaman gudun hijira a asibitin suka kama da wuta mutanen ciki suka ƙone da ransu.
👉
An Israeli airstrike on a hospital compound in central Gaza early Monday sent flames ripping through tents housing displaced people, killing at least four and injuring dozens.
— The Washington Post (@washingtonpost) October 14, 2024
The Israeli military said it was targeting a Hamas command center. https://t.co/7eb7ClmbvL
Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta fitar da rahoton cewa harin da Isra'ila ta kawo asibitin na 'Al-Aqsa Matyrs Hospital' dake birnin Deir al-Balah a arewacin Gaza ya kashe aƙalla Palasɗinawa 4 kuma aƙalla wasu mutum 70 sun samu raunuka, mafi yawansu sun samu munanan raunuka dan haka ana tsammanin samun ƙarin shahidai daga cikin masu raunukan.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira da ransu mai suna Oum Radi ta bayyana ma kafar yaɗa labarai ta Aljazeera cewa "Abinda ya faru shine hayaƙi da wuta suka tashe mu munga wuta na ci tantuna na ƙonewa ta kowane bangare, fashewar Bom ɗin da aka jefo a inda muke rayuwa a farfajiyar asibitin ya razana kowa daga na cikin tantunan har na waje".
Ofishin yaɗa labarai na gwamnatin Gaza ya bayyana cewa wannan shine karo na bakwai a cikin wannan shekarar da Isra'ila ta jefa Bom a asibitin na Al-Aqsa Matyrs Hospital kuma karo na uku a cikin ƴan makonnin nan.
Wakilin kafar yaɗa labarai ta Aljazeera mai a birnin na Deir al-Balah mai suna Hani Mahmoud ya bayyana cewa tantuna 20 zuwa 30 sun ƙone da kuma mutane na maƙale a cikin su".
Mahmoud ya ƙara da cewa "Akwai mutane dayawa a cikin tantunan a lokacin da wutar ta yaɗu a tsakanin tantunan waɗanda ba za a iya ceto rayukan su ba, a halin yanzu muna neman adadi mai yawa na mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon tantunan suna kusa da juna sosai kuma suna a ɗan tsukakken wuri a farfajiyar asibitin".
Ma'aikacin wani gidan Tv da ya ga yadda lamarin ya faru ya bayyana ma kafar yaɗa labarai ta 'The Washington Post' cewa Bom ɗin da Isra'ila ta jefa yasa mazuban gas ɗin girki (Gas Cylinders) sun riƙa tarwatsewa suna kamawa da wuta.
"Wutar ta riƙa ci da saurin gaske ta ƙone tantunan, naga mutum uku suna ƙonewa da idona, wasu gomomi kuma da raunuka, ɗaruruwan iyalai kuma suna gudun ceton rai suna yekuwa, iyaye na neman ƴaƴan su" a cewar shi jami'an bada agaji na Civil Defense sun iya kashe wutar ne bayan tayi mintuna 40 tana ci.
Kafar yaɗa labarai ta 'Washington Post' ta bayyana cewa anga wani faifan bidiyo ya karaɗe kafafen sada zumunta a cikin bidiyon wani mutum na kwance yana ci da wuta da ranshi a gefe guda kuma wasu na kallon shi suna yekuwa.
0 Comments