Jiragen Amurka Da Burtaniya Sun Jefa Boma-Bomai A Yankuna 4 Na Ƙasar Yemen A Jiya Juma'a

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Zuwa yanzu Washington, Burtaniya da kuma haramtacciyar ƙasar Isra'ila sun kai kusan 900 a Yemen dakatar da hare haren goyon bayan Palasɗinu da Yemen take yi.


A jiya juma'a 4 ga watan October jiragen yaƙin Amurka da Burtaniya sun  yi luguden wuta a yankuna 4 na ƙasar ta Yemen ciki har da tashar jirgin sama dake babban birnin ƙasar ta Yemen wato birnin Sana'a da kuma tashar jiragen ruwa  dake birnin Hodeidah.



Wakilin kafar yaɗa labarai ta Almayadeen dake ƙasar ta Yemen ya labarto cewa wuraren da aka kai hare haren sun haɗa da yankunan Dhamar da Al-Bayda dale gabashin ƙasar.


Sai dai ministan yaɗa labarai na gwamnatin ƙasar Hashem Sharaf Al-Din ya jaddada cewa zasu cigaba da kai hare haren goyon baya ga al'ummar Palasɗinu, yayi wannan zantuka ne a lokacin da yake zantawa da kafar yaɗa labarai ta SABA bayan faruwar lamarin.


Hakanan hedkwatar sojin Amurka dake Afirka da ake kira US Central Comman 'CENTCOM' ta fitar da sanarwar cewa sun hari wurare 15 ƴan Houthi dake mulkar kasar Yemen wanda suka kira ƴan koren Iran, a cewar su wannan kokarin dakatar da hare haren goyon bayan Palasɗinawa ne 


👉


Wani Jami'in gwamnatin ƙasar ta Yemen ya bayyana ma kafar yaɗa labarai ta Almayadeen cewa Amurka, Burtaniya da Isra'ila sun kawo hari Yemen aƙalla sau 860 tun da suka fara kai hare haren goyon bayan Palasɗinu, ya kara da cewa a cikin wannan makon kawai Amurka da Burtaniya da Isra'ilar sun kawo masu hari sau 39.


Wannan harin na jita juma'a dai ya biyo bayan gagarumin gangamin da al'ummar ƙasar suka yi na Allah wadai da kashe Sayyid Nasrallah tare da nuna goyon baya ga ƴan muqawama ba Lebanon da Gaza.


Post a Comment

0 Comments