Yadda Palasɗinawa Biyu Suka Kai Harin Jarumta Har Tsakiyar Birnin Tel Aviv



Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Wasu Palasɗinawa biyu sun kai wani harin jarumta har cikin babban birnin Haramtacciyar ƙasar Isra'ila wato Tel Aviv, sun kashe kuma sun raunata da dama.


Kafafen yada labaran Isra'ila sun wallafa cewa mutum takwas maharan suka kashe sannan kuma sun raunata aƙalla mutum 25 da munanan raunuka da ƙanana.


Palasɗinawan biyu sun kai hare haren wurare mabanbanta cikin birnin na Tel Aviv ciki har da tashar jirgin ƙasa dake titin Al-Quds.


Maharan sun yi amfani da bindiga ƙirar Machine Gun.


A ranar Laraba 2 ga watan Oktoba da muka shiga ne rundunar Al-Qassam Brigade ta ƙungiyar Hamas ta fitar da sanarwar ɗaukar alhakin kai harin, inda ta bayyana cewa Palasɗinawan biyu sune Muhammad Rashid Misk da kuma Ahmad Abdul Fattah Al-Haimouni.

👉

Dukan su biyu sun fito ne daga birnin Hebron Dale yammacin gaɓar kogin Jordan sun kutsa cikin birnin Tel Aviv sannan suka ƙwaci bindugun da suka yi amfani dasu a hannun jami'an tsaron Isra'ila.


Muhammad Misk ɗan kimanin shekaru 19 an kashe shi a wurin da suka kai harin, shi kuma Ahmad Al-Haimouni yana da kimanin shekaru 25 ya samu rauni.


Bayan faruwar wannan harin na su ne kuma makaman Iran suka fara sauka cikin Isra'ila a wani harin mayar da martani da Iran ta kai Isra'ilar a ranar ta Laraba wanda ta saka ma suna 'Wa'adul Haqq 2' wato 'True Promise 2' domin daukar fansar Kashe shugaban ofishin siyasa na ƙungiyar Hamas Isma'il Haniyeh, shugaban ƙungiyar Hezbollah Sayyid Hassan Nasrallah da kuma ɗaya daga cikin kwamandojin rundunar kare juyin juya halin Musulunci na Iran mai suna Abbas Nilforoushan.

Post a Comment

0 Comments