Daga - Aminu Sulaiman Bai'a
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kwashe tantuna aƙalla 10,000 a zirin Gaza, hakan ya haifar da zullumi ga Falasɗinawan da suka rasa matsugunansu.
Falasɗinawa a Gaza na ci gaba da fama da yunwa, cututtuka, da kuma tsakanin sanyi, yayin da Isra'ila ke ci gaba da gudanar da gangamin kisan ƙare dangi.
Sama da tantuna 10,000 a sansanin Al-Mawasi da ke Gaza ne suka salwanta sakamakon iska da ruwan sama da aka yi cikin dare a ranar 25 ga watan Nuwamba, lamarin da ya tilasta wa fararen hula da suka rasa matsugunansu ƙaura zuwa yankunan da ke da nisa da gabar teku cikin wani nau'in mawuyacin hali kamar yadda kamfanin dillancin labarai na WAFA ta wallafa.
Jaridar "The National" ta yi hira da mutane da dama waɗanda ambaliyar ruwan ya shafa a yankin sassanin ƴan gudun hijira da ke gabar tekun Gaza. Ga kuma yadda firar ta kasance:
"Teku ya riƙa jan yara, amma mun sami damar kuɓutar da su,” in ji Khaled Idris, wani Bafalasɗine da ke gudun hijira a Mawasi. "Abin da ya same mu jiya bala'i ne na jin ƙai." "Ni da iyalina mun samu nasarar kafa tantinmu a bakin gabar Khan Yunis," in ji Sobhi Shaheen, wata ƴar Gaza da ke gudun hijira. Ta ci gaba, "Tekun ya yi ambaliya sau biyu a wannan shekara - kwanaki 10 na farko da suka wuce sai kuma yau."
Sobhi ta ci gaba da cewa, "Mun yi ƙaura zuwa wani tanti tare da dangin ƴar’uwata a Al-Mawasi, haƙiƙa halin da ake ciki yayi muni. Ruwan ya mayar da yashi ya zamo laka, wanda hakan ya sa ba za a iya motsi ba, kuma sanyin na da tsananin da ba zai yiwu a iya jurewa ba.”
Jaridar "The National" ta ƙara da cewa, yawancin iyalai da suka rasa matsugunansu na dogaro ne da tarkacen kayan da za a yi musu matsuguni, saboda farashin tantuna da fakitin robobin da ake yin su ya yi tashin gwauron zabi.
Mohammed Mushtaha, ɗan gudun hijira ne har sau biyu, na farko daga Shujaiya a birnin Gaza, na biyun kuma daga Rafah, ya bayyana cewa, “Tantinmu sun salwanta sakamakon ambaliya, kuma igiyoyin ruwa sun kwashe komai. Sannan mutane da yawa sun rasa tantunansu. Dole muka gudu saboda tsoron nutsewa. Lamarin ya kasance da matuƙar ban tausayi musamman ga yara, mata, da kuma tsofaffi.”
Mohammed ya ƙara da cewa, "Rayuwarmu tana da wahala sosai, kuma tunanin hakan na da ban tsoro," ya ci gaba da bayani cewa, “Ba zai yiwu ka iya jurewa ba a lokacin da yaronka ke furta maka cewa, ‘Baba, ina jin sanyi,’ alhali ba za ka iya yin komai ba, ko kuma ya sanar maka, ‘Ina jin yunwa,’ kuma ba za ka iya ciyar da shi ba."
Bashar Murad, Daraktan ne na Asibitin Al-Quds, ya shaidawa WAFA cewa kashi 40 cikin 100 na yara a kudancin Gaza na fama da tamowa (wato rashin samun abinci mai gina jiki). Ya kuma bayyana cewa hukumomin mamaya na Isra'ila na hana shigar da kayan agaji.
"A Gaza an kiyasta cewa mutane miliyan 1.9 [tara cikin 10] ne suka rasa matsugunansu, akasarin su mutanen da ke cikin tantunan ne da ba za su iya jure wa guguwar iska ba." Inji Jonathan Crickx, ma'aikacin Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) yayin shaida wa "The National".
Yaɗuwar cututtuka na ƙara zama babbar matsala, kamar yadda Hukumar ba da Agaji da Ayyuka ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta yi gargadi.
"Yanayi mai tsananin sanyi yana haɗuwa da ruwan sama mai ƙarfi da hauhawar matakan ruwa, wanda hakan ke haifar da tarin ƙazanta da kuma sauran cututtuka." in ji UNRWA akan X (wato twitter).
Dokta Murad ya yi gargadi a bayaninsa cewa fararen hula da suka rasa matsugunansu na fama da cututtuka daban-daban na numfashi, musamman tsofaffi da yara, saboda rashin tufafin dumi, da na’urorin dumama, da barguna yayin da sanyin hunturu ke shiga.
A farkon makon nan wakilin dindindin na Masar a Majalisar Dinkin Duniya, Ambasada Osama Abdel Khalek, ya yi gargadin cewa Isra'ila na neman mayar da Gaza zama mara-mazauna tare da tilastawa Falasɗinawa ƙauracewa yankunan kakanninsu.
Tun bayan fara kisan kiyashin da Isra'ila ke yi wa Falasɗinawa a Gaza a watan Oktoban shekarar 2023, sojojin Isra'ila sun kashe sama da mutane 44,000, yawanci kuma mata ne da yara.
Harin bama-bamai da Isra’ila ta kai ya raba kusan ɗaukacin al’ummar Gaza da muhallansu tare da lalata guraren da suka yi wa ƙawanya, waɗanda suka hada da unguwanni, asibitoci, makarantu, masallatai, coci-coci, filayen noma, maƙabarta, da kayayyakin ruwa da lantarki.
#FreePalestine #FromRiverToTheSea
0 Comments