Daga - Mahadi Tukur Almizan
A halin Da Ake Ciki Jirgin ya yada zango an Egypt har zuwa 5 ga watan da muka shiga ba Nuwamba.
Ƙasashe irin su Angola, Slovenia, Montenegro da Malta, duk sun hana jirgin ya yada zango a cikin su saboda yana ɗauke da makamai zuwa Isra'ila.
Jirgin mai ɗauke da tutar kasar Germany mai suna 'MV Kathrin Cargo Vessel ' Yana ɗauke da makamai da boma bomai ya samu izinin yada zango a tashar jiragen ruwa ta ƙasar Egypt ta birnin Alexandria bayan ƙasashe dayawa sun hana shi wannan damar.
Dogaro da bayanan karar da aka shigar akan jirgin a can ƙasar ta Jamus, jirgin na ɗauke da kwantinonin kayan boma bomai da ake kira 'RDX Explosive da suka kai nauyin kilogram dubu 150 an tura wannan kayan ne ga kamfanin ƙere ƙere na sojin Isra'ila waddda ke ƙera makamai, wannan kamfani shine 'Elbit System'.
Ofishin kula da harkokin ruwa na ƙasar Egypt (EMCO) ne ya baiwa wannan jirgi damar yada zango a tashar jiragen ruwan ta Alexandria, kamar yadda bayanan da aka wallafa a shafin yanar gizo na Alexandria.
Wakilan wata ƙungiya ta 'Boycott, Divestment and Sanctions (BDS) sun bayyana cewa "Yada zangon da jirgin yayi a Egypt ya jawo tambayoyi akan me yasa Egypt ta baiwa jirgin dake Safarar kayan ƙera makamai na sojin Isra'ila damar yada zango" wakilan na BDS sun bayyana haka ne ga kafar yaɗa labarai ta Middle East Eye.
Ko a ranar Larabar da ta gabata wasu lauyoyin kare haƙƙin dan Adam 'European Legal Support Center (ELSC) ta shigar da ƙara a kotun Berlin tana neman a dakatar da jirage jigilar makamai, kungiyar ta shigar da ƙarar ne a madadin wasu Palasɗinawa uku daga Gaza.
A cikin zantukan lauyoyin sun bayyana cewa "Isra'ila na amfani da wadannan makaman wajen kashe fararen hula a Gaza da Lebanon tsawon shekara guda".
0 Comments