"Mutum 117 Muka Binne Daga Cikin Ahalinmu" Cewar Wadanda Suka Tsira Da Ransu Na Ahalin Abu Nasr



Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Mutane ƙalilan da suka tsira da ransu daga ahalin 'Abu Nasr Family' bayan kisan kiyashin Isra'ila a Beit Lahia sun baiwa kafar yaɗa labarai ta Almayadeen shaidar gani da ido.


Wadanda suka tsira da ran nasu daga Abu Nasr Family sun tabbatar cewa sojojin mamaya sun kai hari a Beit Lahia ne batare da wani gargaɗi ba.


Yayinda suka zantawa da wakilin Almayadeen sun bayyana cewa ginin da Isra'ila ta hara yana ɗauke da Palasɗinawa ƴan gudun hijira aƙalla 250 "Mun riƙa tafiya tsakanin gawarwakin ababen ƙaunar mu, mun binne mutun 117 daga cikin ahalin mu " a cewar su.

Sojin mamaya na Isra'ila sun share ahalin 'al-Ghabdour Family' a arewacin Gaza kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Almayadeen ta tabbatar.


Da safiyar jiya juma'a a tsakiyar Gaza Palasɗinawa 47 aka kashe wasu gomomi kuma suka samu raunuka mafiyawancin su mata da ƙananan yara, sakamakon Bama baman da Isra'ila ta jefa a Deir al-Balah, sansanin gudun hijira na al-Nuseirat da kuma al-Zawaideh.


Sojojin mamaya sun yi ma gabashin al-Qarara da arewacin Khan Younis da kudancin Gaza ƙawanya.


Wakilin kafar yaɗa labaran ta Almayadeen ya labarto cewa "Samada mutum 150 aka shahadantar a cikin ƴan awannin da suka gabata a cigaba da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a zirin Gaza" wannan na nufin Isra'ila na cigaba da jefa boma bomai a sansanin gudun hijira na Jabalia dake arewacin Gaza.

Post a Comment

0 Comments