Sammacin Kama Natanyahu Bai Wadatar Ba — A Yanke Masa Hukuncin Kisa



Daga - Aminu Sulaiman Ba'a

Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce, sammacin kame firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan yaƙin ƙasar Yoav Gallant bai wadatar ba, sai dai a yanke masu hukuncin kisa saboda munanan laifukan da suka aikata a kan bil'adama.


Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a jiya litinin, a wata ganawa da ya yi da dubban dakarun sa kai na Basij, yayin da sauran miliyoyin ƴan Basij suka riƙa kallonsa kai tsaye ta talabijin.  


Jagoran juyin juya halin Musulunci ya soki lamarin gwamnatin Isra'ilan a Falasɗinu da kuma Lebanon, inda yake cewa, "wawayen sahyoniyawa suna tunanin cewa ta hanyar jefa bama-bamai a gidajen mutane, asibitoci, da kuma wuraren taruwar jama'a su ne nasara alhali a duniya babu wanda ya ɗauki hakan a matsayin nasara."


Sayyid Khamene'i ya kuma jaddada cewa, "maƙiya ba su samu nasara ba, kuma ba za su yi nasara ba a Gaza da Labanon, duk da munanan laifukan yaƙi da suke yi." Jagoran ya ƙara da cewa: "Sammacin kama Netanyahu bai wadatar ba, don haka a yanke masa hukuncin kisa tare da jagororin masu laifi na ƙasar gwamnatin sahyoniya."


Ayatullah Khamene'i ya bayyana laifukan gwamnatin sahyoniyawan a Gaza da Lebanon a matsayin koma baya ga waɗanda suka aikata wannan aika-aika, wanda hakan ya haifar da ƙarfafawa ga ƴan gwagwarmaya. 


Ya ƙara da cewa, jajirtattun matasan Falasɗinawa da na Lebanon, ba tare da la’akari da matsayinsu na zamantakewa ko shiga cikin faɗa ba, amma suke fuskantar hare-haren bama-bamai da barazanar kisa, saboda haka, ba su da wata hanya face faɗa da kuma bijirewa. Don haka, waɗannan wawayen masu laifi, a haƙiƙa, suna ƙara faɗaɗa ƙungiyar ƴan gwagwarmaya ne.”


Sayyid Khamene'i ya jaddada cewa, "faɗaɗa ƙungiyar ƴan gwagwarmaya, wani al'amari ne da ba za a iya kawarwa ba." Yana mai jaddada cewa, "Girman da ƴan gwagwarmaya ke da shi a yanzu, zai ninka a gobe da adadi mai yawa."


A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran ya lissafo cewa, "ƙin amincewa da damar da sauran al'ummomi ke da, da kuma wulakanta su da ƙasashen Turai ke yi a matsayin wani daɗaɗɗiyar manufofin masu mulki don cimma hanƙoronsu."


Ya ƙara da cewa, "Kamar yadda ayoyin Alkur'ani suka nuna, Fir'auna ya raina mutanensa da kuma wulaƙanta su don tabbatar da biyayyarsu, sai dai Fir'auna ya fi masu mulkin Amurka da Turai daraja a halin yanzu, domin kuwa ba wai kawai suna wulaƙanta mutanensu ba ne, suna wulaƙanta jama'arsu ne, kuma su na raina sauran al'ummomi domin su wawashe dukiyarsu da buƙatunsu."


Har ila yau, Ayatullah Khamenei ya bayyana wakilan ƴan mulkin mallaka na cikin gida a matsayin waɗanda suka dace da matsin lambar da ake fama da shi daga waje da kuma yaƙin tunani na azzalumai. Ya ƙara da cewa, “Kamar yadda suka yi a lokacin da aka mayar da harkar man fetur a ƙasar, ya ci gaba da cewa, "su waɗannan jami’an da suka yi daidai da ubangidansu, suna karyata tarihi ne, sanin su da kuma karfin al’umma wajen share wa azzalumai hanya."


Yayin da yake magana kan dakarun Basij na Iran; Jagoran ya ɗauki aƙidar Basij a matsayin wani shamaki, yana mai cewa: "Imani da kai da ya samo asali daga ruhin Basij, yana kawar da makamai masu linzami masu hatsarin gaske na tsarin mamaya, wanda ke da nufin wulakanta su, miƙa kai, da kuma sanya yanke kauna a cikin al'umma. Babu shakka, wannan ruhi da kuma iyawar da za su taso daga gare su, za su yi galaba a kan dukkan manufofin Amurka. Yamma, da kuma gwamnatin Sahayoniya, a cikin ƙasar da kuma cikin mambobin ƙungiyar ƴan gwagwarmaya."


Jagoran ya jaddada cewa: "Ƴan Basij na da imani a manufarsu ta tabbatar da al’ummar Musulunci da wayewa tare da aiwatar da adalci, suna kuma ci gaba ba tare da tsoron mutuwa ba, suna masu sha’awar shahada, saboda waɗannan halaye ne ma Basij suka tabbatar da cewa; wata rana za su kawar da gwamnatin sahyoniya."


Ayatullah Khamenei ya kammala jawabinsa da cewa, "sanin tsare-tsare da Amurka take yi wa ƙasashen yankin da tsayin daka a kansu na daga cikin abubuwan da ke karfafa Basij a fagen siyasa." Inda ya bayyana wani sirri na Amurka da cewa, yanayin da ya dace da Amurka don tabbatar da muradunta a yankin ya shafi ko dai kafa ƴan ta'adda da kama-karya, ko kuma hargitsi da rashin zaman lafiya a cikin ƙasashe. Ko wanne daga cikin waɗannan yanayi guda biyu da suka taso a ƙasar, abokan gaba ne suke yi, kuma dole ne Basij su tsaya a gaba don magance waɗannan makirce-makircen na maƙiya.


____ Husayn Sulaymani — Freedom Fighters Hausa Ng🎙️

27|11|2024

Post a Comment

0 Comments